Sokoto: An ayyana neman wadanda aka gani a bidiyon kone dalibar da ta zagi Annabi

Sokoto: An ayyana neman wadanda aka gani a bidiyon kone dalibar da ta zagi Annabi

  • Rundunar 'yan sandan jihar Sokoto ta fitar da sabon batu, ta ce tana neman wadanda suka kashe Deborah
  • Wannan na zuwa ne jim kadan bayan da aka tasa keyar wasu mutum biyu da aka gano suna da hannu a lamarin
  • Ya zuwa yanzu, ana ci gaba da ganin cece-kuce a bangarori da yawa a fadin kasar nan tun bayan kisan wacce ta zagi Annabi

Jihar Sokoto - Rundunar ‘yan sanda a Sokoto ta ayyana neman wadanda suka yi ikrarin kashe Deborah a wani faifan bidiyo, TheCable ta ruwaito.

A ranar 12 ga watan Mayu, wasu fusatattun matasa sun far wa Deborah, dalibar Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari tare da kone ta kurmus kan wasu kalamai da ta yi na batanci ga Annabi Muhammad SAW.

Faifan bidiyo da ke nuna yadda aka kashe dalibar da dukan tsiya da sanduna kafin a kone ta, ya yadu a shafukan sada zumunta.

Kara karanta wannan

Matasa sun nuna fushinsu yayin da wata Naomi Goni ta kara ɓatanci ga Annabi SAW, an kama 3

'Yan sanda na daukar mataki kan kisan Deborah
Sokoto: An ayyana neman wadanda aka gani a bidiyon kone dalibar da ta zagi Annabi | Hoto: punchng.com, dailytrust.com
Asali: Facebook

A daya daga cikin faifan bidiyon, wasu mutane sun dauki alhakin kashe Deborah, yayin da suke nunawa kansu a kyamara dayansu na rike da kwalin ashana da aka yi amfani da ita wajen cinna wa marigayiyar wuta.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Lamarin dai ya janyo cece-kuce da kuma tofin Allah tsine a fadin kasar nan kuma rundunar ‘yan sanda a Sokoto, ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da hannu a kisan.

A ranar Litinin, wata kotun majistare da ke zamanta a Sokoto ta tasa keyar mutanen biyu a gidan yari, kamar yadda rahotanni suka tabbatar.

Da yake bayar da karin haske kan lamarin, Sanusi Abubakar, kakakin rundunar ‘yan sandan Sokoto, a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, ya yi kira ga jama’a da su bayar da bayanai kan wadanda ake zargin, rahoton Channels Tv.

Kara karanta wannan

Kisan Deborah: Kungiya ta nemi a kamo limamin BUK bisa zargin halasta jinin Bishop Kukah

Ya ce:

“Rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto a karkashin jagorancin kwamishinan ‘yan sanda, CP Kamaldeen Kola Okunlola fdc, ta bayyana cewa ana neman wadanda ake zargin da aka gani a cikin faifan bidiyo.
“Rundunar tana amfani da wannan kafar ne domin jaddada kudirinta na cafke wadanda ake zargin. Tuni dai rundunar ta dasa jami'anta na sirri kuma tana ci gaba da neman wadanda ake zargin .
"An umurci jama'a da su ba 'yan sanda hadin kai tare da kai rahoton duk wani motsi ga rundunar ko wani jami'in tsaro a yankinsu."

Tirkashi: Lauyoyi 34 a gaban kotu don kare daliban da suka kashe wacce ta zagi Annabi

A wani labarin, rundunar ‘yan sanda ta gurfanar da wasu mutane biyu da ake zargi da hannu a kisan dalibar Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari da ke Sokoto, Deborah Samuel, da ta durawa Annabi ashariya.

Wadanda ake zargin – Bilyaminu Aliyu da Aminu Hukunchi – wadanda kuma daliban kwalejin ne, an gurfanar da su a gaban wata kotun majistare da ke jihar a ranar Litinin, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Sokoto: Yadda lauyoyi 34 suka bayyana a kotu don kare daliban da suka kashe wacce ta zagi Annabi

A cewar rahoton farko na ‘yan sanda, an gurfanar da wadanda ake zargin ne a gaban kuliya sakamakon tayar da tarzomar da ta kai kisa da kone dalibar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel