Hotunan Gida Da Mota Da Aka Ba Wa Iyayen Deborah, Ɗalibar Da Aka Kashe Kan Ɓatanci a Sokoto

Hotunan Gida Da Mota Da Aka Ba Wa Iyayen Deborah, Ɗalibar Da Aka Kashe Kan Ɓatanci a Sokoto

  • Chibuzor Chinyere, Babban Faston Cocin Omega Power Ministry, (OPM), ya gwangwaje iyayen Deborah Samuel Yakubu, dalibar da aka kashe a Sokoto da kyautan motar hawa da gida.
  • Bayan ya sa an kawo su Jihar Rivers a jirgin sama, Faston ya ce da kudin baiko da sadaka da yan cocinsa suka biya ne ya siya wa iyayen Deborah gida da motan
  • An kashe Deborah ne a harabar Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari da ke Sokoto a ranar 12 ga watan Mayu bayan zarginta da furta kalaman batanci kan Annabi (SAW)

Port Harcourt - Chibuzor Chinyere, babban faston cocin Omega Power Ministry, (OPM), ya mika kyautan gida da mota ga iyalan Deborah Samuel Yakubu, dalibar da aka kashe a Sokoto kan batanci ga Annabi (SAW). The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

Rade-radin takara a APC na kara karfi, Goodluck Jonathan ya yi kus-kus da Mamman Daura

An yi wa Deborah, dalibar aji na 2 a Kwalejin Ilmi ta Shehu Shagari a Sokoto duka da sanduna kafin nan aka cinna mata wuta a harabar makarantar a ranar 12 ga watan Mayu.

Hotunan Gida Da Mota Da Aka Ba Wa Iyayen Deborah, Ɗalibar Da Aka Kashe Kan Ɓatanci a Sokoto
Gida da coci ta bawa iyayen Deborah Samuel a PortHarcourt. Hoto: The Cable.
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Duk da cewa wasu sun yi tir da kisar da aka yi mata a Najeriya da kasashen ketare, an yi zanga-zanga a Sokoto na neman ganin an sako wadanda ake zargi da hannu a kisar ta.

Babban faston na OPM ya gabatar da gida da motan ne a ranar Talata, yayin da ya hadu da iyayen Deborah a Port Harcourt, babban birnin Jihar Rivers.

An dakko iyalanta ne cikin jirgin sama daga Jihar Niger zuwa Rivers.

Da Kudin baiko da sadaka aka siya gida da motar

A cewar babban faston na OPM, kudin baiko da sadaka na mambobin cocinsa ne aka yi amfani da shi wurin siyan gida da motar 'don kabu-kabu' ga iyalan Deborah.

Kara karanta wannan

Innalillahi: 'Yan Boko Haram sun yanka manoma 45 a wani sabon harin Borno

Ga hotunan a kasa:

Hotunan Gida Da Mota Da Aka Ba Wa Iyayen Deborah, Ɗalibar Da Aka Kashe Kan Ɓatanci a Sokoto
Gidan da Fasto ya bawa iyayen Deborah. Hoto: The Cable
Asali: Twitter

Hotunan Gida Da Mota Da Aka Ba Wa Iyayen Deborah, Ɗalibar Da Aka Kashe Kan Ɓatanci a Sokoto
Moar da Fasto ya bawa mahaifin Deborah domin ya rika kabu-kabu. Hoto: The Cable.
Asali: Twitter

Hotunan Gida Da Mota Da Aka Ba Wa Iyayen Deborah, Ɗalibar Da Aka Kashe Kan Ɓatanci a Sokoto
Mahaifin Deborah tare da fasto a Portharcourt. Hoto: The Cable.
Asali: Twitter

Hotunan Gida Da Mota Da Aka Ba Wa Iyayen Deborah, Ɗalibar Da Aka Kashe Kan Ɓatanci a Sokoto
Mahaifiyar Deborah tare da fasto a Jihar Rivers. Hoto: The Cable.
Asali: Twitter

Hotunan Gida Da Mota Da Aka Ba Wa Iyayen Deborah, Ɗalibar Da Aka Kashe Kan Ɓatanci a Sokoto
Iyayen Deborah suna saka hannu kan takardar gida da mota da fasto ya basu. Hoto: The Cable.
Asali: Twitter

'Batanci: Ba Za Mu Lamunci Kashe Kiristoci a Bauchi Ba Da Sunan Zagin Annabi, CAN Ta Ja Kunnen Musulmi

A wani rahoton, Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) ta nuna bacin ranta dangane da zargin wata da batanci da aka yi a Jihar Bauchi, inda ta ja kunne akan cewa ba za ta lamunci kisa da sunan batanci ba, Leadership ta ruwaito.

Kungiyar ta CAN kalubalanci gwamnati da kuma jami’an tsaro akan su yi gaggawar daukar matakin da ya dace akan tozarta kundin tsarin mulkin da ake yi kafin gagarumin tashin hankali ya barke wanda za a kasa dakatar da shi.

A wata takarda wacce shugaban kungiyar na reshen Jihar Kaduna, Rabaran Joseph John Hayab ya saki, ya ce CAN ta kula da yada ake amfani da sunan batanci a arewacin Najeriya ana halaka wadanda ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda ba su karasa halakawa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel