Sheikh Gumi: An Sha 'Zagin' Annabi Lokacin Yana Raye, Amma Bai Kashe Kowa Ba Saboda Hakan

Sheikh Gumi: An Sha 'Zagin' Annabi Lokacin Yana Raye, Amma Bai Kashe Kowa Ba Saboda Hakan

  • A lokacin rayuwarsa, an sha zagin Annabi Muhammad (SAW) amma bai taba kai wa wani hari ba, a cewar Sheikh Ahmad Gumi
  • Fitaccen malamin addinin musuluncin ya ce annabi bai yi ramuwa ko kashe masu zaginsa ba domin ba ya son a yi masa lakabi da mai kisa
  • Gumi ya yi wannan tsokacin ne bayan kisar wata daliba kirista mace, Deborah Samuel Yakubu da aka yi kan zarginta da batanci ga Annabi Muhammad (SAW)

Fitaccen malamin addinin musulunci, Ahmed Gumi, ya ce wadanda ba musulmi ba sun sha zagin Annabi Muhammad (tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi) a lokacin da ya ke raye, amma bai taba kowa ba ko kashe masu yi masa batanci.

Sheikh Gumi ya bayyana hakan ne yayin wani zaman karatu da ya yi a masallacin Juma'a a Kaduna, rahoton Premium Times.

Kara karanta wannan

2023: Matasan CAN Sun Bayyana Abin Da Za Su Yi Wa Duk Ɗan Takarar Da Bai Fito Fili Ya Yi Allah Wadai Da Kisan Ɗalibar Da Ta Zagi Annabi Ba

Sheikh Gumi: An Sha 'Zagin' Annabi Lokacin Yana Raye, Amma Bai Kashe Kowa Ba Saboda Hakan
Sheikh Gumi: An Sha 'Zagin' Annabi Lokacin Yana Da Rai, Amma Bai Kashe Kowa Ba. Hoto: Premium Times.
Asali: UGC

Annabi kai kashe munafikai da ke zaginsa ba a lokacin da ya ke da rai, Gumi

Malamin, kamar yadda ya furta a wata bidiyo da Ahmad Bulama ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce manzon Allah bai yi ramuwa ko kashe wadanda suke cutar da shi da zaginsa ba don kada a rika yayatawa cewa Annabi na kashe abokansa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya yi wannan furucin ne yayin da ya ke magana kan kashe daliba kirista yar makarantar Shehu Shagari ta Ilimi a Sokoto kan zarginta da furta kalaman batanci ga Manzon Allah.

Ya bayyana cewa hanyar da ta fi dacewa musulmi su nuna kaunarsu ga Annabi Muhammad (SAW) shine bin koyarwarsa sau da kafa a maimakon kashe mutane kan wasu abubuwa.

Duk wanda ya kashe wanda suka yi alkawarin zaman lafiya tare bai zai ji kanshin aljanna ba nisanta shekarar 40, Gumi

Kara karanta wannan

Kannywood: Na Yi Nadamar Shiga Rikicin Ali Nuhu Da Adam Zango, General BMB

A cewarsa, musulmi da kirista sun amince su zauna a kasa daya, don haka Najeriya kasa ce da ake hukunci da kundin tsarin mulki ba shari'a ba.

"Don haka, duk wanda ya kashe wani da ba musulmi ba da suka yi alkawarin zama lafiya, ba zai ji kamshin aljanna nisanta shekara 40 ba," in ji shi.

Gumi, yayin da ya ke cewa babu wanda aka bawa dama a dauki doka a hannunsa a musulunci, ya yi kira ga malaman addinin musulunci su rika koyar da mabiyansu ilimi mai nagarta a maimakon tunzura su aikata 'munanan' ayyuka.

"Idan muna tunanin kashe Deborah, zai sa mutanen ba ba musulmi ba su dena zagin annabin mu, ya nuna muna mafarki ne," ya ce.

Ƙungiyar CAN Za Ta Yi Gagarumin Zanga-Zanga Na Ƙasa Kan Kisar Deborah Samuel

A wani rahoton, kungiyar Kiristoci ta Najeriya, CAN, ta bukaci a yi zanga-zanga na kasa bisa kisar da aka yi wa Deborah Samuel, dalibar aji 2 na Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari da ke Sokoto, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Deborah Samuel: Ƴan Najeriya Sun Yi Wa Ɗan Tsohon IGP Martani Kan Kalamansa Game Da Kisar Ɗalibar Sokoto Da Ta Zagi Annabi

Shugaban CAN, Rabaran Olasupo Ayokunle, cikin wasikar da ya aike wa dukkan shugabannin kungiyar, ya bukaci kiristoci su yi zanga-zangar lumana a harabar cocinsu a ranar Lahadi 22 ga watan Mayun 2022.

Ya yi kirar ne bayan kisa da kona wata daliba da fusatattun matasa suka yi bayan zarginta da furta kalaman batanci ga Annabi Muhammadu (SAW).

Asali: Legit.ng

Online view pixel