Da duminsa: Ana tsaka da rikicin addini, 'yan bindiga sun kai hari cocin Kukah, sun kwashe fastoci da wasu

Da duminsa: Ana tsaka da rikicin addini, 'yan bindiga sun kai hari cocin Kukah, sun kwashe fastoci da wasu

  • Miyagun 'yan bindiga dauke da makamai sun kutsa cocin Rabaren Kukah inda suka sace fastoci biyu da wasu mutum biyu
  • Mummunan al'amarin ya faru ne a daya daga cikin majami'un Kukah da ke Gidan Maikabo a karamar hukumar Kafur ta jihar Katsina
  • Wannan lamarin na faruwa ne ana tsaka da rikicin addini tare da kai wa majami'ar Kukah farmaki kan daliba Deborah da aka zarga da batanci ga Annabi

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

'Yan bindiga a safiyar Laraba sun balle daya daga cikin majami'un babban Rabaren na Sokoto, Matthew Hassan-Kukah, The Punch ta rahoto hakan.

An tattaro cewa, 'yan bindigan dauke da makamai sun sace wasu fastoci biyu da wasu mutum biyu a cocin katolika ta St. Patrick, Gidan Maikambo a karamar hukumar Kafur ta jihar Katsina.

Kara karanta wannan

Innalillahi: 'Yan Boko Haram sun yanka manoma 45 a wani sabon harin Borno

Manyan majami'un Kukah sun bazu a jihohin Katsina, Zamfara da Kebbi.

Daraktan sadarwa na Catholic Diocese na Sokoto, Rabaren Christopher Omotosho, ya tabbatar da aukuwar lamarin a safiyar Laraba.

Da duminsa: 'Yan bindiga sun kai hari cocin Kukah, sun kwashe fastoci da wasu
Da duminsa: 'Yan bindiga sun kai hari cocin Kukah, sun kwashe fastoci da wasu. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce an kai farmaki majami'arsu kuma har yanzu babu labarin da suka samu kan inda aka yi da wadanda aka sace.

Omotosho ya ce, "Da tsakar daren yau, 25 ga watan Mayun 2022, 'yan bindiga sun shiga majami'ar mu ta St. Patrick, Gidan Maikambo, karamar hukumar Kafur ta jihar Katsina.
"An sace babban faston Rabaren Fada Stephen Ojapa, MSP, da mataimakinsa Oliver Okpara da wasu yara maza biyu a gidan.
"Har yanzu babu karin bayani kan inda suke. Ku taimaka ku saka su a ddu'a domin su dawo cikin aminci."

A ranar 14 ga watan Mayu, fusatattun matasa masu zanga-zanga sun kone tare da tarwatsa cocin da Kukah ke shugabanta a Sokoto bayan ya yi Allah wadai da kisan da aka yi wa Deborah Samuel, dalibar da ta yi batanci ga Annabi.

Kara karanta wannan

AK9Train: Miyagu sun tuntubi kakakin Sheikh Gumi, sun ba FG wa'adin kwana 7 ko su aiwatar da nufinsu

Masu zanga-zangar sun kone wani daga cikin sashin ginin cocin Kukah kuma sun bankawa wata bas wuta a farfajiyar.

Rikicin addinin na Sokoto ya kara gaba ina ya shiga wasu sassan jihohin Bauchi da Abuja a kwanakin da suka gabata yayin da jami'an tsaro da wasu gwamnonin arewa suka ja kunne kan tashin hankula.

AK9Train: Miyagu sun tuntubi kakakin Sheikh Gumi, sun ba FG wa'adin kwana 7 ko su aiwatar da nufinsu

A wani labari na daban, miyagun da suka sace sama da fasinjoji 60 a jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna a ranar 28 ga watan Maris, 2022 suna barazanar halaka dukkan wadanda ke hannunsu matukar gwamnatin tarayya ba ta cika sharuddansu ba, HumAngle ta rahoto.

Wannan na kunshe ne a wani sautin sakon murya wanda jaridar Desert Herald ta samu inda 'yan ta'addan suka yi magana da Tukur Mamu, mai magana da yawun Sheikh Mahmud Gumi, fitaccen malamin addinin Islama na garin Kaduna.

Kara karanta wannan

Siyasa: 'Yan daba sun farmaki 'yan jarida a taron kamfen din wani gwamnan APC

A tattaunawar, mai magana da yawun 'yan ta'addan ya ce lokacin da gwamnatin tarayya ta same su, sun bayyana cewa suna bukatar a saki 'ya'yansu, wadanda su takwas ne kuma daga nan sai su bayyana wadanda za su saki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel