Zanga-zanga bayan zagin Annabi: Tambuwal ya sassauta dokar hana fita a Sokoto

Zanga-zanga bayan zagin Annabi: Tambuwal ya sassauta dokar hana fita a Sokoto

  • Gwamnatin jihar Sokoto ta sassauta dokar hana fita da ta sanya a jihar biyo bayan barkewar rikici
  • Wannan na zuwa ne bayan da aka samu dan lafawar rikicin da ya kai zanga-zangar mazauna Sokoto
  • Asalin tushen rikicin ya samo asali tun bayan kam wasu dalibai da sauka kashe wacce ta zagi Annabi a Sokoto

Sokoto - Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya sanar da sake duba dokar hana fita ta sa'o'i 24 da aka kafa a jihar tun bayan tashin hankalin da ya biyo bayan zanga-zangar da wasu mazauna jihar suka fara a ranar Asabar.

A cewar wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar Isah Galadanci ya fitar a safiyar ranar Litinin, gwamnati ta sake duba dokar hana fita daga sa’o’i 24 zuwa daga magariba zuwa wayewar gari.

Kara karanta wannan

Zagin Annabi a Sokoto: Masu zanga-zanga sun farmaka tare da lalata coci 2 a Sokoto

Gwamna Tambuwal ya sassauta dokar hana fita a jihar Sokoto
Zanga-zanga bayan zagin Annabi: Tambuwal ya sassauta dokar hana fita a Sokoto | Hoto: dailytrust.com
Asali: Facebook

Ya ce an yi hakan ne don baiwa mazauna jihar damar gudanar da harkokinsu na rayuwa kamar yadda kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya ya tanada, Punch ta ruwaito.

The Guardian ta ruwaito yana cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“A ci gaba da bayanin da Jami’an tsaro suka yi a Jihar, Gwamnan Jihar, Rt Hon Aminu Waziri Tambuwal, CFR Mutawallen Sokoto, ya bayar da umarnin sassauta dokar hana fita ta sa’o’i 24 da aka kafa a cikin babban birnin Sokoto.
“A yanzu dokar hana fita za ta kasance daga magariba zuwa wayewar gari a cikin garin Sokoto. Wannan kenan don baiwa mutane damar yin kasuwanci na halal da sauran hanyoyin rayuwa.
“Gwamnati, ta shawarci mutane da su wanzar da zaman lafiya a wannan lokaci, domin ba za ta lamunci karya doka da oda a jihar ba.”

Bayan zaman kotu, an tura wadanda suka kashe dalibar da ta zagi Annabi magarkama

Kara karanta wannan

Dokar kulle: Bishop Kukah ya yabawa matakin Tambuwal, ya karyata batun kai hari gidansa

A wani labarin, rundunar ‘yan sanda ta gurfanar da wasu mutane biyu da ake zargi da hannu a kisan dalibar Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari da ke Sokoto, Deborah Samuel, da ta durawa Annabi ashariya.

Wadanda ake zargin – Bilyaminu Aliyu da Aminu Hukunchi – wadanda kuma daliban kwalejin ne, an gurfanar da su a gaban wata kotun majistare da ke jihar a ranar Litinin, Daily Trust ta ruwaito.

A cewar rahoton farko na ‘yan sanda, an gurfanar da wadanda ake zargin ne a gaban kuliya sakamakon tayar da tarzomar da ta kai kisa da kone dalibar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel