'Batanci: Ƴaƴan Mu Ba Za Su Sake Zuwa Makaranta Ba, In Ji Iyayen Deborah

'Batanci: Ƴaƴan Mu Ba Za Su Sake Zuwa Makaranta Ba, In Ji Iyayen Deborah

  • Alheri Emmanuel, mahaifiyar Deborah, dalibar Kwalejin Ilimi ta Sokoto da aka kashe saboda batanci ga Manzon Allah (SAW) a ta ce sauran 'ya'yanta ba za su sake zuwa makaranta ba
  • Alheri ta kuma ce ba ta da wani bukata daga hannun kowa sannan ba su da niyyar zuwa kotu ko shigar da korafi a wani wuri domin sun bar wa Ubangiji komai a hannunsa
  • Emmanuel Garba, mahaifin marigayiya Deborah, a bagarensa ya ce babu wani jami'in gwamnati da ya tuntube shi kuma shi ya biya N120,000 aka dako masa gawarsa yarsa daga Sokoto zuwa Neja

Sokoto - Mahaifiyar Deborah Samuel Yakubu, dalibar da aka kashe a Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari a Sokoto, Alheri Emmanuel ta ce sauran yayanta ba za su sake zuwa makaranta ba.

Alheri ta bayyana hakan ne cikin wata, hawaye da jimami a hira da aka yi da ita bayan mutuwar yar nata a Sokoto kamar yadda The Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

2023: Matasan CAN Sun Bayyana Abin Da Za Su Yi Wa Duk Ɗan Takarar Da Bai Fito Fili Ya Yi Allah Wadai Da Kisan Ɗalibar Da Ta Zagi Annabi Ba

'Batanci: Ƴaƴan Mu Ba Za Su Sake Zuwa Makaranta Ba, In Ji Iyayen Deborah
Zagin Annabi: Ƴaƴan Mu Ba Za Su Sake Zuwa Makaranta Ba, In Ji Iyayen Deborah
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ba ni da wata bukata; ba na son komai amma abu daya da na sani shine yaya na ba za su sake zuwa makaranta ba," a cewar ta.

Ba za mu tafi kotu ba, kuma babu wanda ya tuntube mu, mahaifin Deborah

A bangarensa, Emmanuel Garba, mahaifin Deborah a hirar da The Punch ta yi da shi a ranar Lahadi ya ce ya biya N120,000 kudin mota domin dauko gawar yarsa daga Jihar Sokoto zuwa Neja.

Garba ya ce ba zai tafi kotu ba yana mai cewa kuma cewa kawo yanzu babu wani jami'in gwamnati da ya tuntube shi duk da kisar da aka yi wa yarsa.

Ya ce:

"Har yanzu babu wanda ya tuntube ni kan lamarin. Babu wanda ya kira ni; ni na tafi da kai na. Na tafi ofishin CID na roke su don a bani gawar in birne ta domin idan na bar shi a wurin zai lalace. Sun kai ni dakin ajiye gawa, na yi wasu rubuce-rubuce sannan aka bani gawar."

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi: An Sha 'Zagin' Annabi Lokacin Yana Raye, Amma Bai Kashe Kowa Ba Saboda Hakan

"Ni na biya kudin motar dauko gawar, an caje ni N120,000 domin shine mafi sauki da aka caje ni don mafi yawancin mutane ba su son daukar gawa."

Garba, wanda mai gadi ne a hukumar ruwa ta Jihar Neja ya ce matarsa ta kamu da rashin lafiya, ya kara da cewa yanzu aka gama mata allura.

2023: Ba Za Mu Zaɓi Duk Ɗan Siyasan Da Bai Fito Filli Ya Yi Alla Wadai Da Kisan Deborah Ba, Matasan CAN

A bangare guda, Kungiyar Kiristocin Najeriya, reshen matasa (YOWICAN) ta yi barazanar cewa ba za ta zabi duk wani dan siyasa da bai yi alla wadai da kisar da wasu suka yi wa Deborah Yakubu ba kan zarginta da zagin Annabi (SAW), Nigerian Tribune ta rahoto.

Belusochukwu Enwere, shugaban na YOWICAN na kasa, ya yi kira ga jami'an tsaro su binciko wadanda suka yi kisar da kuma wadanda ke lalata dukiyoyin al'umma a Sokoto yayin zanga-zangar da aka yi na baya-bayan nan don neman sakin wadanda aka kama kan zargin kisa Deborah.

Kara karanta wannan

Kannywood: Na Yi Nadamar Shiga Rikicin Ali Nuhu Da Adam Zango, General BMB

Asali: Legit.ng

Online view pixel