Sarkin Musulmi Ya Yi Zazzafan Martani Kan Kisar Harira Da Yaranta 4 Da 'Yan Ta'adda Suka Yi a Anambra

Sarkin Musulmi Ya Yi Zazzafan Martani Kan Kisar Harira Da Yaranta 4 Da 'Yan Ta'adda Suka Yi a Anambra

  • Sarkin musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya koka akan kisan Harira Jibrin da yaranta hudu a Isulo da ke karamar hukumar Orumba ta Arewa a Jihar Anambra da wasu ‘yan bindiga su ka yi
  • Sultan wanda ya ke shugabantar Jama’atul Nasril Islam, ya nuna rashin jin dadinsa akan mummunan lamarin inda ya ce kisan rashin hankali ne kuma kauyanci ne
  • Ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya akan ta jajirce wurin ganin ta gano ‘yan bindigan da su ka yi bakin aikin a maboyarsu don daukar matakin da ya dace

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Sokoto - Alhaji Sa’ad Abubakar III, Sarkin musulmi ya koka akan kisan Harira Jibrin, da yaranta hudu a Isulo cikin karamar hukumar Orumba ta Arewa da ke cikin Jihar Anambra da wasu ‘yan bindiga su ka yi.

Sultan wanda ke shugabantar Jama’atul Nasril Islam, JNI ya yi suka kwarai akan kisan inda ya ce rashin hankali da kauyanci ne, The Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kashe-kashe a Kudu maso Gabas: Ku tsammanci martani mai tsauri daga gareni, Buhari ga 'yan IPOB

Ya Isa Haka: Sarkin Musulmi Ya Magantu Kan Kisar Harira Da Yaranta 4 Da 'Yan Ta'adda Suka Bindige a Anambra
Sarkin Musulmi Ya Yi Allah wadai Da Kisar Harira Da Yaranta 4 Da 'Yan Ta'adda Suka Suka Yi a Anambra. Hoto: The Punch.
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya bukaci gwamnati ta yi gaggawar daukar matakin da ya dace

Ya roki Gwamnatin Tarayya akan ta dage wurin ganin ta gano ‘yan bindigan da su ka yi aika-aikan a maboyarsu cikin gaggawa, Daily Trust ta ruwaito.

Sultan din shugaba ne ga duk Musulman Najeriya kuma ya bayyana alhininsa kwarai akan kisan rashin imanin da ake ta yi a kasar nan saboda rashin tsaro.

The Punch ta ruwaito yadda wani bangare na takardar da JNI ta saki ya zo kamar haka:

“A maimakon Shugaban kungiyar, Mai girma Sultan na Sokoto, Alhaji(Dr.) Muhammad Sa’adu Abubakar, CFR, mni, Jama’atul Nasril Islam ta yi alawadai da rashin hankali, kauyanci da kuma mummunan kisan da aka yi wa wata Harira Jibrin; mace mai ciki da yaranta guda hudu a Isulo da ke karamar hukumar Orumba ta Arewa da ke Jihar Anambra.”

Kara karanta wannan

Rayuwar dan Adam ta yi arha a Najeriya: CAN ta yi Alla-wadai da kisan Fatima da yaranta a Anambra

Sarkin musulmi ya ce ya kamata gwamnati ta tauna tsakkuwa don aya ta ji tsoro

A cewarsa:

“Lamarin kari ne akan kashe-kashen da ake ta yi wa mutane da dama, musamman musulman jihohin Kudu maso Gabashin Najeriya. Abin alawadai ne yadda ake ta nuna rashin imani ta hanyar halaka rayuka a kasar nan.
“Cikin radadi, JNI ta kula da yadda musulman kirki 'yan kasuwa har da dabbobinsu su ke fama a yankin. Wannan alama ce ta tsana da rashin imanin da ake nuna musu. JNI ta na ganin lokaci ya yi da ya kamata gwamnati ta yi kokarin daukar mataki.”

Ya kara da cewa ya kamata gwamnati ta zage damtse wurin hukunta duk wadanda ke da hannu a kashe-kashen Kudu maso Gabas kafin lokaci ya kure.

Ya ci gaba da cewa wajibi ne gwamnati ta dauki mataki ta hanyar ratsa dazuka da maboyun ‘yan ta’addan don gano su. Kuma hakan ne zai sanya a tauna tsakkuwa don aya ta ji tsoro.

Kara karanta wannan

Kuma dai: ‘Yan bindiga sun farmaki ofishin yan sanda a Anambra, sun kona motoci

'Yan IPOB Sun Kashe Wata Mata Mai Juna Biyu, Yaranta 4 Da Wasu 'Yan Arewa 6 a Anambra

Tunda farko, kun ji cewa a ranar Lahadi, Mayakan IPOB sun halaka wata mata mai juna biyu, yaranta 4 da kuma wasu mutane 6, wadanda duk ‘yan arewa ne da ke zama a Jihar Anambra, Daily Trust ta ruwaito.

Sun halaka matar, wacce ke dauke da juna-biyu da yaranta ne a Isulo, karamar hukumar Orumba ta Arewa a jihar.

Kashe-kashen wani sabon salon ta’addanci ne da ‘yan IPOB su ke kan yi wa wadanda ba asalin ‘yan jihar ba, kuma har sojoji da ‘yan sanda ba su bari ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel