Tirkashi: Lauyoyi 34 a gaban kotu don kare daliban da suka kashe wacce ta zagi Annabi

Tirkashi: Lauyoyi 34 a gaban kotu don kare daliban da suka kashe wacce ta zagi Annabi

  • Rahotannin da ke iso mu sun bayyana yadda wasu lauyoyi suka bayyana gaban kotu domin kare daliban da suka kashe Deborah Samuel
  • An ruwaito a baya yadda wasu dalibai suka kashe wata yarinyar da ta durawa Annabi SAW ashawar a kafar WhatsApp
  • Yau dai an zauna a kotu, an tura daliban biyu zuwa magarkama bisa zarginsu da daukar doka hannu

Sokoto - Rundunar ‘yan sanda ta gurfanar da wasu mutane biyu da ake zargi da hannu a kisan dalibar Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari da ke Sokoto, Deborah Samuel, da ta durawa Annabi ashariya.

Wadanda ake zargin – Bilyaminu Aliyu da Aminu Hukunchi – wadanda kuma daliban kwalejin ne, an gurfanar da su a gaban wata kotun majistare da ke jihar a ranar Litinin, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kisan Deborah: Kungiya ta nemi a kamo limamin BUK bisa zargin halasta jinin Bishop Kukah

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya bayar da rahoton cewa lauyoyi 34 ne suka bayyana domin kare daliban biyu da ake zargi da kashe dalibar da ta zagi Annabi, inji rahoton Sahara Repoerters.

Yadda aka kaya a kotu
Sokoto: An tura wadanda suka kashe dalibar da ta zagi Annabi zuwa magarkama | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

A cewar rahoton farko na ‘yan sanda, an gurfanar da wadanda ake zargin ne a gaban kuliya sakamakon tayar da tarzomar da ta kai kisa da kone dalibar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bayan wadanda ake zargin sun ki amsa laifin da ake tuhumar su da su, dan sanda mai shigar da kara, Insifekta Khalil Musa, ya bukaci kotun da ta dage karar domin baiwa ‘yan sanda damar kammala bincike.

Sai dai lauyoyin wadanda ake kara karkashin jagorancin Farfesa Mansur Ibrahim, wadanda ba su yi adawa da bukatar tsagin masu shigar da kara ba, sun roki kotun da ta bayar da belin mutanen biyu.

Hakzalika, sun bayar da misali da sashe na 157, 161(a,f) da 164 na shari’ar laifuka ta jihar Sakkwato, da kuma shashe na 36 (5) na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya na 1999 da aka yi wa kwaskwarima.

Kara karanta wannan

'Batanci: Jakadiyar Birtaniya Ta Ce Dole a Hukunta Waɗanda Suka Kashe Ɗalibar Sokoto

Sai dai kotun ta dage sauraron karar zuwa wani lokaci wanda za a sanar da lauyoyin daga baya.

Don haka ta umurci wadanda ake tuhuma da a tsare su a gidan gyaran hali na Sokoto.

Kisan Deborah: Kungiya ta nemi a kamo limamin BUK bisa zargin halasta jinin Bishop Kukah

A wani labarin, kungiyar kare hakkin bil’adama ta HURIWA, a ranar Litinin, ta nemi jami'an SSS da su kama babban limamin Jami’ar Bayero Kano, Sheikh Abubakar Jibril bisa zargin tunzura al’ummar Musulmi kan Bishop Matthew Hassan-Kukah.

HURIWA, a cikin wata sanarwa da kodinetan kungiyar na kasa, Emmanuel Onwubiko, ya fitar, ta ce an ga Jibril a wani faifan bidiyo da ake zargin yana gaya wa dimbin mabiyansa musulmi da su nemi adireshin gidan Kukah, kuma su far masa, rahoton Punch.

A ranar Alhamis din da ta gabata ne wasu suka yi wa wata dalibar Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari da ke Sokoto ruwan duwatsu tare da kona gawarta saboda durawa Annabi Muhammad SAW ashariya.

Kara karanta wannan

Sokoto: Tambuwal ya umarci a yi bincike kan kashe dalibar kwalejin da ta zagi Annabi

Asali: Legit.ng

Online view pixel