Zagin Annabi: Dole A Yi Adalci Kan Kisar Deborah Yakubu, In Ji Amina Mohammed

Zagin Annabi: Dole A Yi Adalci Kan Kisar Deborah Yakubu, In Ji Amina Mohammed

  • Amina Mohammed, Mataimakiyar Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci a yi adalci bisa kashe Deborah Yakubu
  • Amina ta yi wannan kirar ne cikin wani rubutu da ta wallafa a shafinta na Twitter tana mai cewa bai kamata a yi amfani da addini wurin tada rikici ba
  • Mataimakiyar Sakaren na UN ta kuma mika sakon ta'aziyya ga iyalan marigayiya Deborah sannan ta kuma yi addu'ar Ubangiji ya ji kan marigayiyar

Mataimakiyar Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, UN, Amina Mohammed, ta ce ya zama dole a yi adalci game da kashe Deborah Samuel Yakubu, wacce aka halaka sannan aka kona a Sokoto.

Mohammed, wacce ta yi wannan kirar a cikin wani wallafa da ta yi a shafinta na Twitter a ranar Talata ta ce, bai dace a rika 'yi wa addini fasarar da bai dace ba domin tada rikici.'

Kara karanta wannan

Batanci ga Annabi: Gwamnati ta cire takunkumi a Sokoto, ta haramta zanga-zanga

Zagin Ananabi: Dole A Yi Adalci Kan Kisar Deborah Yakubu, In Ji Amina Mohammed
'Batanci: Dole A Yi Adalci Kan Kisar Deborah Yakubu, In Ji Amina Mohammed. Hoto: Vanguard.
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ya zama dole a yi adalci bisa mummunan kisar matashiya Deborah Yakubu a Najeriya. Bai dace a rika yi wa addini fasara wurin tada rikici ba a yayin da zaman lafiya suke koyarwa.
"Ina addu'a ga iyalanta kuma ina addu'ar Ubangiji ya yi mata rahama," a cewar sakon da ta wallafa.

Idan za a iya tuna wa cewa Deborah, daliba a Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari a Sokoto ta gamu da ajalinta ne, a hannun fusatattun gungun mutane a makarantar a ranar Alhamis kan zargin batanci ga Annabi (SAW).

Rundunar yan sandan Jihar Sokoto ta gurfanar da mutane biyu, Bilyaminu Aliyu da Aminu Hukunci, gaban Kotun Majistare da ke jihar, kan zarginsu da hannu a aikata laifin.

Amma, tuni an fara zanga-zanga bayan kama wadanda ake zargi din, wanda tunda farko sun musanta tuhumar da ake musu.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Hatsarin mota ya rutsa da dan takarar gwamnan APC a Abuja

'Batanci: Atiku Ya Ce Ba Shine Ya Wallafa Rubutun Sukar Kashe Ɗalibar Sokoto a Shafinsa Ba

A wani rahoton, Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP ya nisanta kansa daga yin ala-wadai akan kisan Deborah Samuel.

Deborah dalibar aji biyu ce a kwalejin ilimi ta Shehu Shagari da ke Jihar Sokoto, kuma kirista ce, an halaka ta ne bisa zarginta da yin batanci ga Annabi Muhammad SAW.

Sai dai Atiku ya yi wata wallafa a Twitter inda ya ce:

“Babu adalci dangane da kisan muguntar da aka yi mata. An halaka Deborah Yakubu kuma wajibi ne a kwatar mata hakkinta akan wadanda su ka halaka ta. Ina mai yi wa ‘yan uwanta da kawayenta ta’aziyya.”

Kara karanta wannan

Matata Da ƳaƳana Sun Saba Haɗuwa Su Lakaɗa Min Duka, Magidanci Mai Neman Saki

Asali: Legit.ng

Online view pixel