'Mun bar wa Allah' Iyayen ɗalibar da ta zagi Annabi a Sokoto sun yi magana bayan binneta

'Mun bar wa Allah' Iyayen ɗalibar da ta zagi Annabi a Sokoto sun yi magana bayan binneta

  • Iyayen ɗalibar da ta yi kalaman Batanci ga Annabi Muhammad (SAW) sun yi magana kan abinda ya faru a Sakkawato bayan binne gawarta
  • Mahaifin Debora Samuel ya bayyana yadda direbobi suka guje shi kafin ya sami wanda ya ɗakko gawar zuwa Neja kan N120,000
  • Sai dai a jawabinsu, sun ce sun ɗauki kaddara kuma duk abin da za'a yi ba zai dawo musu da ɗiyarsu ba

Niger - Mahaifin Debora Samuel, wacce aka kashe kan zargin ɓatanci a Sakkwato, Emmanuel Garba, ya bayyana cewa iyalansa sun ɗauki abun da da ya faru a matsayin kaddara daga Allah.

A ranar Asabar aka birne gawar Debora a mahaifarta da ke Tungan Magajiya. ƙaramar hukumar Rijau a jihar Neja, kamar yadda The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Ministan albarkatun man fetur ya janye daga takarar shugaban kasa a 2023

A wata zantawa da Dailypost, Garba, ya ce iyalansa sun shiga ƙunci bisa kisan Debora, amma ya ce ba abin da zasu iya yi game da lamarin.

Iyayen Debora Samuel.
'Mun bar wa Allah' Iyayen ɗalibar da ta zagi Annabi a Sokoto sun yi magana bayan binneta Hoto: The Nation
Asali: UGC

Garba ya kuma bayyana yadda ya biya N120,000 na ɗakko gawarta daga Sakkwato zuwa Neja bayan ya fahimtar da gwamnati ta barshi ya birne gawar ɗiyarsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mahaifin Debora ya ce:

"Ba zamu iya yin komai ba illa mu ɗauki abun da sauki a matsayin muƙaddari daga Allah. Mun bar komai a wurin Allah. Ni da kaina na je ɗakko gawarta domin na mata jana'iza saboda barinta ɗakin aje gawa ba zai dawo mun da ita ba."
"Da naje na haɗu da jami'an gwamnati kuma na fahimtar da su bani dama na ɗauki gawarta zuwa gida, suka amince. Da naje inda aka aje ta sun bukaci na sa hannu a takardu kuma na yi, nan take suka bani ita."

Kara karanta wannan

Sokoto: Wani Malami ya yi alkawarin daukar nauyin iyayen ɗalibar da ta zagi Annabi, yace sun gama wahala a duniya

"Sai da na biya N120,000 na motar ɗakkota bayan direbobi da yawa sun ƙi yarda da aikin, hakan ta faru ne saboda yanayin da gawar ke ciki, kowane direba na nema sai yaƙi banda ɗaya"

A cewarsa, gwamnati ta bukaci na bar gawarta a can amma ya gaya musu cewa su yi hakuri su barshi ya yi wa ɗiyarsa gatan ƙarshe na birne ta.

Shin ita ce kaɗai diyarsu?

A nata ɓangaren mahaifiyarta, Alheri Emmanuel, tace Debora yar su ce ɗaya daga cikin 'ya'ya Bakwai da Allah ya azurta su da ita.

Ta ce:

"Ba abinda zan ce, na gode wa Allah da kuma kokarin ku, na miƙa zuciyata ga Allah, ina fatan ya bani ƙarfin jurewa, ba abinda zamu ce."
"Saboda abun da ya faru ba zan sake tura ƴaƴana karatu inda za'a kashe kuɗi da yawa ba. A kan karatunta, sauran yan uwanta sun shiga yanayi a na su karatun don ba zamu iya ɗaukar nauyin su a lokaci ɗaya ba."

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Dumi: Yan bindiga sun banka wuta a Kamfanin rarraba wutar lantarki, sun tafka ɓarna

A wani labarin kuma Abin da Malamai suka faɗa wa gwamna Tambuwal a wurin taron bayan kashe ɗalibar da ta zagi Annabi a Sokoto

Malaman da suka halarci taro da gwamna Tambuwal sun shawarci gwamnati kan yadda za'a dakile faruwar ɗaukar doka a hannu nan gaba.

Gwamnan ya kira taro da Malamai ne bayan rikicin da ya yi sanadin kashe ɗaliba da ake zargin ta yi batanci ga Annabi SAW.

Asali: Legit.ng

Online view pixel