Siyasar Najeriya
Allah ya yi wa dan majalisar jihar Kogi mai wakiltar mazabar Yagba a majalisar jihar, Jimoh Ommiata rasu. Ya rasu ne a ranar Litinin a wani asibiti da ke Legas.
Za a ji Jam’iyyar LP ta karbe kujerar ‘dan majalisar wakilan tarayya na shiyyar Kaura a jihar Kaduna. Donatus Mathew wanda ya taba zama ‘Dan acaba ya ci zabe.
Yanzu muke samun labarin cewa, tsohon gwamnan jihar Edo ya yi nasara a zaben sanata da aka gudanar a mazabarsa, inda ya banke abokin hamayyarsa na yankin a PDP.
Ƙawo yanzun da aka ayyana sakamakon zaben shugaban kasa daga kananan hukumomi 17 cikin 20 na jihar Legas, Peter Obi na LP na kan gaban Bola Tinubu na APC .
Sanata Abdullahi Adamu, Shugaban jam'iyyar APC na kasa ya gaza kawo wa jam'iyyarsa ta APC kujerar sanata na yankin Nasarawa ta Yamma a zaben ranar Asabar 25.
Gwamna Ben Ayade na jihar Cross River da takwaransa Ifeanyi Ugwuanyi na jihar Enugu sun sha kaye a zaben sanata da aka yi a ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairu.
APC tayi nasara a zaben 'Yan majalisa a Katsina, PDP ta rasa duka Sanatoci 3 na jihar. Kanal Abdulaziz Yar’adua mai ritaya zai zama ‘Dan majalisar dattawa.
Abba Ganduje bai yi nasarar zama ‘dan majalisar tarayya ba, Honarabul Abdulkadir Tijjani Jobe zai koma majalisa a karo na biyar bayan lashe zaben 'dan majalisa.
Babban jami’in da ke tattara zaben jihar Delta bai gamsu da sakamakon zaben Ika ta Arewa maso gabas ba. 30, 105 aka tantance, amma mutum 31, 681 suka yi zabe
Siyasar Najeriya
Samu kari