2023: Jerin Sunayen Yan Takarar Gwamna A PDP Da Suka Ziyarci Wike

2023: Jerin Sunayen Yan Takarar Gwamna A PDP Da Suka Ziyarci Wike

 • Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya karbi bakuncin wasu yan siyasan Najeriya a gidansa da ke Port Harcourt a ranar Talata, 6 ga watan Satumba
 • Bakin sun kasance yan takarar gwamna na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a fadin Najeriya, ciki harda dan marigayi Janar Sani Abacha, Muhammad
 • Ganawar da suka shafe kimanin awanni uku suna yi cikin sirri ba zai rasa nasaba da shirin yan takarar na son ganin sun yi nasara a babban zaben 2023 ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Rivers – A kokarinsu na son ganin sun yi nasara a babban zaben 2023, wata tawaga ta yan takarar gwamna karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) su 18 sun ziyarci Gwamna Nyesom Wike a jihar Ribas.

Majiyoyi sun bayyana cewa yan takarar sun gana da Wike ne a gidansa da ke Port Harcout, babban birnin jihar ta Ribas a ranar Talata, 6 ga watan Satumba.

Kara karanta wannan

Hotuna: Lamiɗo, Da Wasu Yan Takarar Gwamna 16 Na Jam'iyar PDP Sun Sa Labule da Wike

Yan takarar gwamna na PDP
2023: Jerin Sunayen Yan Takarar Gwamna A PDP Da Suka Ziyarci Wike Hoto: Lere Olayinka
Asali: Facebook

An tattaro cewa ganawar da suka yi cikin sirri ya shafe tsawon kimanin awanni uku (8 na dare zuwa 11 na dare).

Ga jerin sunayen yan takarar da jihohin da suka wakilta a kasa:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

 1. Jihar Jigawa - Mustapha Sule Lamido
 2. Jihar Kaduna - Isa Ashiru
 3. Jihar Katsina - Yakubu Lado Danmarke
 4. Jihar Plateau - Caleb Mutfwang
 5. Jihar Nasarawa - Hon. David Ombugadu
 6. Jihar Kebbi - Janar Aminu Muhammad Bande mai ritaya
 7. Jihar Benue - Titus Uba
 8. Jihar Sokoto - Sa'idu Umar
 9. Jihar Borno - Mohammed Ali Jajeri
 10. Jihar Yobe - Alhaji Shariff Abdullahi
 11. Jihar Kwara - Yahman Abdullahi
 12. Jihar Kano - Muhammad Abacha
 13. Jihar Lagos - Olajide Adediran
 14. Jihar Niger - Alhaji Isah Liman Kantigi
 15. Jihar Ogun - Segun Showunmi
 16. Jihar Cross River - Senator Sandy Onor
 17. Jihar Delta - Sheriff Oborevwori
 18. Jihar Rivers - Siminialayi Fubara

Kara karanta wannan

2023: Jerin Manyan Yan Kannywood 3 Da Ke Neman Takara A Jam'iyyar ADP

Duk Masu Shirya Yadda Zasu Halakani, Su Zasu Fara Mutuwa, Wike

A wani labarin, Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya bayyana cewa ana barazanar da ake masa sakamakon rikicin cikin gida na PDP inda yace masu son kashe shi zasu mutu kafin su kai ga halaka shi.

Gwamnan yayin jaddada cewa tun 1999 jihar na bada goyon baya a fannin kuri'u da kudi fiye da sauran jihohi. A cewarsa:

"Ya isa haka kan yadda ake amfani da watsi da 'yan PDP."

Asali: Legit.ng

Online view pixel