Tinubu da Atiku Sun Yi Wa Mata Alkawarin Fiye da Abin da Suke Nema a Gwamnati

Tinubu da Atiku Sun Yi Wa Mata Alkawarin Fiye da Abin da Suke Nema a Gwamnati

  • ‘Dan takarar shugaban kasa karkashin inuwar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar yace zai dama da mata da matasa
  • Asiwaju Bola Tinubu da Sanata Kashim Shettima sun yi alkawarin fiye da 35% na mukamai ga matasa da kuma mata
  • Mata suna neman a ware masu 35% na kujeru, shi kuwa Dino Melaya yace Atiku zai yi masu fiye da haka a mulki

Abuja - Atiku Abubakar mai harin takara a jam’iyyar hamayya ta PDP ya yi alkawarin kashi 40% na kujerun da zai raba za su tafi ne ga mata da matasa.

A ranar Litinin dinnan Punch ta rahoto Atiku Abubakar yana cewa idan ya samu dama, zai tafi da mata da matasa wajen ganin kawo cigaba a Najeriya.

‘Dan takaran ya yi wannan bayani ne ta bakin Kakakin kwamitinsa na kamfe watau Sanata Dino Melaye a wajen wani taro da aka shirya a garin Abuja.

Kara karanta wannan

ASUU: An kai makura, gwamnatin Buhari ta yi sabon batu, ta fadi kokarinta a dinke matsalar ASUU

A wajen taron, Titi Abubakar ta jaddada cewa Mai gidanta zai cika alkawarin da ya yi na rabawa matasa da mata akalla 40% na mukamai a gwamnatinsa.

Atiku zai yi da mata – Dino, Titi

Melaye yake cewa a lokacin da mata ke neman 35% na kason kujeru da mukamai, Atiku Abubakar ya sha alwashin zai ba su 40% idan ya yi nasara a 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana haka sai aka ji gidan VOA Hausa sun rahoto Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da abokin takararsa, Sanata Kashim Shattima sun yi irin wannan alkawari.

Asiwaju
'Dan takaran APC, Asiwaju Bola Tinubu: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

Da mu za ayi mulki - Shugabar matan APC

‘Yan majalisar dokoki na APC a jihohin Arewacin Najeriya sun shirya wani taro a karshen makon jiya, a nan suka jaddada goyon bayansu ga ‘yan takaran.

An rahoto mataimakiyar shugabar mata ta jam’iyyar APC ta kasa, Zainab Ibrahim tana cewa fiye da 35% na kujeru za su je ga mata idan Tinubu ya ci zabe.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Shugaban 'yan sanda ya magantu kan yiwuwar yin zabe a shekara mai zuwa

Da mu za ayi – Matasan da ke tare da APC

Legit.ng Hausa ta tuntubi Aminu Ahmad Gadagau wanda matashi ne wanda ake damawa da su a APC a Kaduna, yana cikin masu goyon bayan Tinubu.

Aminu Ahmad Gadagau yace idan aka lura da yadda matasa da mata ke taka rawar gani wajen yi wa Bola Tinubu kamfe, za a fahimci da su za ayi mulki.

Gadagau ya kara da cewa abin da Tinubu da Shettima suka yi a lokacin suna mulki ya kara tabbatar da cewa za a ba sa’o’insa mukamai idan APC ta ci zabe.

...haka ne

Shi ma Sahabi Sufyan wanda ya nemi kujerar shugaban matasan APC na kasa yace ‘dan takaransu mutum ne mai zakulo wadanda suka san kan aiki.

Sufyan yace daga lokacin da Bola Tinubu ya yi gwamna a Legas zuwa yanzu, ya gina manyan ‘yan siyasa, wadanda har gobe da-dama suna tare da shi.

Kara karanta wannan

Manyan 'Yan Siyasa 10 Masu Karfin Tasiri a Zabukan 2023 Dake Gabatowa

Masoyin na Tinubu yace gwamnatin APC tayi abin da ya fi na baya wajen ba matasa mukamai, sannan an kawo dokar da ta ba matasa damar takara.

Dino Melaye v Femi Fani-Kayode

Kafin nan kun samu labari Femi Fani-Kayode ya bada shawarar a cafke Dino Melaye a dalilin maganar da ya yi kan Gwamnonin PDP da Iyorchia Ayu.

Sanata Melaye wanda Fani-Kayode ya kira karen Bukola Saraki da su Atiku Abubakar ya caccaki tsohon Ministan kasar a Twitter da Facebook.

Asali: Legit.ng

Online view pixel