Dan Takarar Shugaban Kasan APC Ya Ba Wadanda Ambaliyar Ruwa Ya Shafa Tallafi a Jigawa
- Dan takarar shugaban kasa a APC, Asiwaju Bola Tinubu ya ba da tallafin miliyoyi ga mazauna jihar Jigawa
- An samu faruwar wata mummunar ambaliyar ruwa a Jigawa, lamarin da ya jawo asarar dukiyoyi da dama
- An samu faruwar ambaliyar ruwa a jihohin Najeriya da dama a daminar bana, an yi asarar dukiya da rayuka
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Jihar Jigawa - Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a zaben 2023, Asiwaju Bola Tinubu ya ba da tallafin Naira miliyan 50 ga jama'ar da ambaliyar ruwa ta shafa a jihar Jigawa, Vanguard ta ruwaito.
Tinubu ya sanar da ba da wannan tallafi ne jim kadan bayan ganawarsa ta jaje da gwamna Muhammad Badaru na Jigawa, a birnin Dutse ranar Talata 6 ga watan Satumba.
Dan takarar na APC ya yi kira ga jama'a da su dukufa da rokon Allah da ya yaye wannan musiba ta ambaliyar ruwa a jihar da ma kasa baki daya.
A kalaman Tinubu:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"Duk da cewa na yiwa wadanda lamarin ya shafa jaje ta hannun gwamnanku, amma na ji ya cancanta na zo da kaina domin in yi muku jaje."
Tinubu ya samu rakiyar jiga-jigan APC
Ba Tinubu kadai bane ya zo Jigawa, ya samu rakiyar gwamna Simon Lalong na jihar Filato da shugaban jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Adamu.
Hakazalika da shugabar mata ta jam’iyyar APC ta kasa Dr Betta Edu da tsohon shugaban hukumar EFCC Nuhu Ribadu da dai kusoshin APC, rahoton Daily Nigerian.
Gwamna Badaru ya karbi bakuncin dan takarar shugaban kasan, ya kuma ce ziyarar tasa ta taimaka matuka ga wadanda ambaliyar ruwan saman ta shafa.
A cewar gwamna Badaru:
“A baya Tinubu ya kirani a waya ya jajanta min a lokacin da aka samu faruwar ambaliya ta farko a Kafin-Hausa, ya sake kira na a lokacin da hakan ya faru a Hadejia, Gumel da Malammadori.
“Bugu da kari, makwanni biyu da suka gabata, lokacin da makamancin wannan lamarin ya faru a Birnin-Kudu, Gwaram da Dutse, musamman Karnaya, Tinubu ya sake kira na.
“Gashi a yau, ya yanke shawarar zuwa da kansa duk da irin karancin lokaci da yake dashi domin ya jajantawa jama’armu game da mumunar ambaliyar ruwa da ta afka musu a baya-bayan nan.”
Za a fuskanci ambaliyar ruwa a watannin Augusta da Satumba a Najeriya, NiMet
A baya kunji cewa, Najeriya zata fuskanci gagarumar ambaliyar ruwa a watannin Augusta da Satumba, kamar yadda hukumar kula da yanayi, NiMet ta tabbatar.
Shugaban NiMet, Farfesa Mansur Bako Matazu, ya bayyana hakan a wani shirin gidan talabijin na Channels TV a ranar Litinin.
Yace cibiyar ta bada shawarwari daban-daban akan ambaliyar ruwa wanda 'yan Najeriya suka ki kiyayewa.
Asali: Legit.ng