Shugabannin APC da Dumbin Magoya Baya Sun Sauya Sheka Zuwa PDP A Sakkwato

Shugabannin APC da Dumbin Magoya Baya Sun Sauya Sheka Zuwa PDP A Sakkwato

  • Sakataren APC da mataimakin Ma'ajiyi a wata Gundumar jihar Sakkwato sun sauya sheƙa zuwa jam'iyyar PDP
  • Jami'in hulɗa da jama'a na PDP, Sahabi Sanyinnawal, yace bayan haka akwai wasu jiga-jigan APC da dandazon magoya baya da suka bi sahunsu
  • Wannan na zuwa ne yayin da PDP a matakin ƙasa ke fama da rikicin cikin gida musamman kan murabus ɗin Ayu

Sokoto - Sakataren jam'iyyar APC a gundumar Dingyadi-Badawa, ƙaramar hukumar Bodinga, jihar Sokoto, Ummarun Hassan, da mataimakin ma'ajiyi, Manu Abubakar, sun sauya sheka zuwa PDP.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa jami'in hulɗa da jama'a na jam'iyyar PDP, Sahabi Sanyinnawal, shi ne ya tabbatar da sauya sheƙar jiga-jigan biyu a wata sanarwa.

Sauya sheka a Najeriya.
Shugabannin APC da Dumbin Magoya Baya Sun Sauya Sheka Zuwa PDP A Sakkwato Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Yace kakakin jam'iyyar APC na Barno Akamawa, da wasu mambobi huɗu, Shehu Abubakar, Sani Modi, Sanusi Imam da Bello Alhaji sun tattara baki ɗaya magoya bayansu zuwa PDP.

Kara karanta wannan

Lamari Ya Kara Dagule Wa APC, Ɗaruruwan Mambobinta Sun Sauya Sheka Zuwa Jam'iyyar PDP

Shugaban PDP a jihar Sakkwato, Bello Goronyo, wanda ya yi maraba da masu sauya sheƙar ya tabbatar musu da cewa ba za'a tauye musu damarmakinsu na Mambobi ba kuma ba za'a nuna musu banbanci ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ina mai tabbatar muku da cewa za'a ɗauke ku dai-dai da kowa a matsayin cikakkun mambobin jam'iyyar mu mai girma, PDP," inji shi.

Da yake alƙawarin tafiya da kowa a harkokin jam'iyya, Goronyo ya roki sabbin mambobin da su zuba kwarewarsu ta siyasa da jajirce wa wajen ganin PDP ta kai ga nasara a babban zaɓen 2023.

Meyasa suka sauya sheka zuwa PDP?

Kwamishinan Filaye da Gidaje na jihar Sakkwato, Aminu Bala Bodinga, wanda ya fito daga ƙaramar hukuma ɗaya da masu sauya shekar, yace yana da yaƙinin salon jagorancin gwamna Tambuwal ya ja hankalinsu zuwa PDP.

Kwamishinan ya ƙara da yi wa waɗan da suka sauya shekan fatan Alheri a dukkan lamurransu na siyasa da suka sanya a gaba.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: An Tsige Shugaban Jam'iyyar APC Daga Kujerarsa a Jihar Arewa

A wani labarin kuma Lamiɗo, Da Wasu Yan Takarar Gwamna 16 Na Jam'iyar PDP Sun Sa Labule da Wike

Yan takarar gwamna a jihohin Najeriya akalla 17 a inuwar PDP sun dira Patakwal, sun shiga ganawa da Wike.

Wata majiya ta tabbatar da cewa an fara taron kofa kulle da misalin ƙarfe 8:00 na daren ranar Talata 6 ga watan Satumba, 2022.

Asali: Legit.ng

Online view pixel