Matasan Najeriya
Gwamnatin tarayyan Najeriya ta nemi afuwar yan Najeriya kan wahalar karancin takardun Naira, inda ta ce nan da sabuwar shekarar 2024 za a kawar da matsalar.
Gwamnatin jihar Kano ta gurfanar da matashi mai suna Musbahu Yau a gaban babbar kotun jihar kan zargin caka wa abokinsa wuka a ciki har sai da hanji ya fito.
Wani dan Najeriya ya hau Facebook ya amayar da abin da ke cikinsa yayin da ya ke neman afuwar matarsa bayan dirkawa budurwarsa ciki yayin da ita ma ta ke da shi.
Wata kyakykyawar daliba ta fashe da kuka bayan wani matashi ya ba ta kyautar naira dubu 20. Dama dai dalibai ta jima tana zullumin yadda za ta biya kudin makarantar.
Rahotanni sun nuna wani ango mai jiran gado, Abraham Basif. ya riga mu gidan gaskiya yayin da ya rage kwanaki uku kacal kafin ranar ɗaura aurensa a karshen mako.
Wasu yan Najeriya sun nuna rashin jin daɗinsa bisa yadda Gwamna Fubara ya sa hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya tsakaninsa da Ministan Abuja, Nyesom Wike.
Wani bidiyo ya nuno makudan kudi da wani direban tasi ya tsinta a cikin motarsa. An rahoto cewa wani fasinjan Port Harcourt ne ya manta da shi a cikin motar.
Bidiyon wani matashi da ya sauya rayuwarsa daga matukin babur zuwa babban dan kasuwa tare da kera katafaren gidan kansa ya dauka hankalin jama’a a soshiyal midiya.
Wata ‘yar Najeriya da ta gina gidan ta a cikin wata bakwai kacal ta burge mutane da dama a yanar gizo. Ta wallafa bidiyo na katafaren ginin mai kyakkyawan tsari.
Matasan Najeriya
Samu kari