Labaran tattalin arzikin Najeriya
Kamfanin simintin Dahiru Mangal ya ƙaryata jita-jitar siyar da buhu kan farashin N6,000 kamar yadda ake yaɗawa a kafofin sadarwa inda ya ba al'umma shawara.
Gwamnatin jihar Neja ta sha alwashin bullo da sababbin shirye-shiryen tallafi domin magamce wahalhalun tsadar rayuwar da mutane ke fama da su a jihar.
Ewi na Ado-Ekiti, Oba Rufus Adejugbe ya haramta kungiyoyin 'yan kasuwa da ke tsauwalawa mutane kan tsadar kaya tare da kayyade farashin kayan abinci.
Yayin da ake dab da kammala kwanaki 10 na zanga zanga, darajar kuɗin Najeriya ta ƙara farfaɗowa a kasuwar bayan fage da farashin gwamnatin Najeriya.
Zinariya wata kadara ce mai kima wacce za ta iya inganta ajiyar kudin ketare, rage dogaro ga rancen kasashen waje. Mun tattaro kasashe 10 mafi samar da shi a Afrika.
Mele Kyari, shugaban NNPC, ya ce kamfanin bai karya wata doka a mu’amalarsa da abokan hulda ba, don haka a daina alakanta su da zagon kasa na tattalin arziki.
A yayin da aka shiga kwana na takwas a zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa, almajira sun roki matasa da su dakata haka, sakamakon rashin abinci a gare su.
Gwamnatin Kano ta gayyaci kungiyar 'yan kasuwar jihar domin gano dalilin tsadar kayayyaki tun bayan fara zanga-zanga a ranar Alhamis, lamarin da ya sa jama'a kokawa.
An ce wa'adin biyan wani bashi da Dangote ya karba zai cika karshen watan Agusta, saboda hakan ya fara shirin sayar da 12.75% na hannun jarin matatarsa.
Labaran tattalin arzikin Najeriya
Samu kari