Attajirin Bakano Abdul Samad Ya Zama Na Hudu a Jerin Masu Kudi a Nahiyar Afrika

Attajirin Bakano Abdul Samad Ya Zama Na Hudu a Jerin Masu Kudi a Nahiyar Afrika

  • Attajirin Bakano ya sake tsallake matsayi mai girma, ya zama mutum na hudu mafi kudi a nahiyar Afrika gaba daya
  • Wannan na zuwa ne yayin da kamfaninsa ya samu ribar kudade masu yawa a shekarar da ta gabata ta 2022
  • Abdul Samad na daga cikin attajiran Najeriya da ke samun habakar dukiya a cikin shekarun nan na baya

Abdul Samad Rabiu ya karbi mukamin mutum na hudu mafi dukiya a nahiyar Afrika, inda ya banke attajirin kasar Masar, Nassef Sawarus watanni bayan zama na biyu a Najeriya.

A baya kunji yadda Abdul Samad ya kara samun duniya a 2022, inda ya zama na biyu a Najeriya bayan Aliko Dangote, inda ya banke Mike Adenuga daga mukamin.

Wannan bayanin dai na zuwa ne daidai da rahoton jaridar Forbes mai bin diddigin arzikin attajirai a duniya.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Da Yiwuwan A Daina Taron Kamfe, Babban Dan takarar Shugaban Kasa Ya Kamu Da Sabuwar Nauyin Cutar Korona

Abdulsamad ya zama na biyu a attajiran Afrika
Attajirin Bakano Abdul Samad Ya Zama Na Biyu a Jerin Masu Kudi a Nahiyar Afrika | Hoto: naijacelebrities.net
Asali: UGC

A cewar rahoton NairaMetrics, Rabiu ya samu karin akalla $2.4bn a shekarar da ta gabata, inda dukiyarsa ta karu daga $4.9bn zuwa $7.6bn ya zuwa lokacin hada wannan rahoton.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Abdul Samad ne attajiri na biyu mafi kudi a Najeriya

A yanzu haka shine mutum na hudu da ya fi kowa kudi a Najeriya bayan wasu biyu da attajiri dan Najeriya kuma dan jiha daya dashi wato Dangote wanda shine na daya.

Masu bin bayan Dangote a yanzu wasu attajirai ne su ma ‘yan kasa daya, Afrika ta Kudu wato Johann Rupert da Nicky Oppenheimer.

A yanzu haka, Abdul Samad ya dara Nassef ne da kudade masu yawam domin Nassef na da $7.3bn a yanzu, shi kuwa yana da $7.6bn.

Akasarin kudaden da Nassef ya mallaka sun samo ta harkallarsa na kamfanin Adidas da OCI N.V, wanda hakan yasa ya zama attajiri a yankin Afrika ta Arewa da ma duniyar Labarawa.

Kara karanta wannan

2023: Fitaccen Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Kamu Da Cutar COVID19

Meye ya habaka dukiyar Abdul Samad?

An ruwaito cewa, kudaden attajirin Bakanon sun samu ne ta hanyar samar da kayayyaki da kamfaninsa na BUA Group ke yi.

BUA dai wani kamfani ne fitacce a nahiyar Afrika da ke samar kayayyakin abinci da gine-gine da dai sauran abubuwan rayuwa nay au da kullum.

Kuma kamfanin daya daga cikin masu gogayya da na Dangote a nahiyar Afrika, domin suna samar da kayayyaki iri daya.

A baya an bayyana muku yadda Dangote ya ci cibar makudan kudade a karshen shekara, amma duk da haka 2022 ta zo masa da raguwar dukiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel