Gobara Ta Kone Gonar Tsohon Jakadan Najeriya, Ta Lalata Bishiyoyi Masu Darajar Miliyoyi

Gobara Ta Kone Gonar Tsohon Jakadan Najeriya, Ta Lalata Bishiyoyi Masu Darajar Miliyoyi

  • Tsohuwar jakadiyar Najeriya ta shiga jimami yayin da gonarta ta kama da wuta a wata mummunar gobara da ta tashi
  • Hotuna sun nuna yadda gonar ta kone kurmus ta koma toka, an rasa miliyoyin kudade daga gonar kwakwan
  • Da take magana, mai gonar ta bayyana halin da ta shuga da kuma yadda take tsammanin samun riba a baya

Jihar Ogun - Wata gobara da sanyin safiya ta yi kaca-kaca da wata gona da ke yankin Onipepe a karamar hukumar Obafemi-Owode a jihar Ogun, inda ta lalata bishiyoyin kwakwa masu darajar miliyoyin Naira.

An ruwaito cewa, gonar mallakin wata tsohuwar jakadiyar Najeriya ce a kasar Zambia/Malawi, Mrs Folake Marcus Bello.

Majiya ta shaidawa Daily Trust cewa lamarin ya faru ne da sanyin safiyar ranar Talata, kuma ta cinye hekta 10 na gonar kwakwan mai suna Folake B Farm.

Kara karanta wannan

Da Gaske ICPC Ta Kama Dan Takarar Gwamnan APC a Sokoto Kan Badakalar Biliyan N12? Aliyu Sokoto Ya Fayyace Gaskiyar Lamari

Gonar babban jami'ar gwamnati ta kone kurmus
Gobara Ta Kone Gonar Tsohon Jakadan Najeriya, Ta Lalata Bishiyoyi Masu Darajar Miliyoyi | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

A cewar rahoton, akalla bishiyoyi 500 ne suka kone da kuma wasu kayayyaki masu darajar gaske da ke cikin gonar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Meye sanadiyyar tashin gobarar?

Ya zuwa yanzu dai ba a san dalilin aukuwar gobarar ba, amma an ce gobarar ta shafe akalla awanni hudu tana ci kafin daga bisani a kashe ta.

Lokacin da manema labarai suka ziyarci gonar a ranar Alhamis, an ga komai ya kone kurmus zuwa toka.

Manajan gona, Mrs Adesola Adebayo ta bayyana cewa, ta samu kira ne da misalin karfe 4:30 na yamma, inda aka sanar da ita cewa gonar na ci da wut, lamarin da yasa ta taso da gaggawa zuwa wurin.

A cewarta, lokacin da ta iso ta tarar da mutanen kauyen sun gaza kashe wutar saboda yawanta, kana tace hunturu ne sanadiyyar ta'azzara wutar ta kara yawa.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An Tafka Asara, Gobara Ta Lakume Dukiyar Miliyoyin Naira a Babban Birnin Jiha

Mai gona ta tabbatar da faruwar lamarin

Ta da ta je tabbatar da faruwar lamarin, tsohuwar jakadiyar ta ce, ta gaza cewa komai lokacin da ta samu labarin abin da ya faru da gonarta.

Ta kuma bayyana cewa, ta zuba makudan miliyoyi a gonar, amma ta rasa komai da ke ciki a yanzu, Daily Post ta ruwaito.

Hakazalika, ta koka da wannan asarar, inda tace a yanzu haka tana dab da girbi ne lokacin da lamarin ya faru, tana tsammanin samun ribar makudan kudade.

A wani bangare guda, gobara ta lakume kayan miliyoyin Nairori a wata kasuwar kayan karafan mota a jihar Oyo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel