CBN Ya Aika Sakonnin Tes Ga ’Yan Najeriya Kan Batun Tsofaffin Naira, Ya Gargadi Bankuna

CBN Ya Aika Sakonnin Tes Ga ’Yan Najeriya Kan Batun Tsofaffin Naira, Ya Gargadi Bankuna

  • Babban bankin Najeriya ya fara tura sako ga dukkan ‘yan Najeriya game da lamarin tsoffin kudin Naira da ke yawo a kasar
  • Bankin ya shawarci ‘yan Najeriya da kada su ysaya wata-wata, su gaggauta kai kudadensu bankuna kafin 31 ga Janairun bana
  • A bangare guda, bankin ya gargadi bankuna da sauran cibiyoyin kudi da su daina koron sabbin kudi, su zuba su a na’urorin ATM

Najeriya - Babban Bankin Najeriya (CBN) ya fara tura sakonni tuni ga ‘yan Najeriya game da cikar wa’adin da aka dibarwa tsoffin kudin kasar.

Bankin ya shawarci ‘yan kasar da su gaggauta kai kudadensu zuwa banki ba sai sun jira ranar karshe ta cikar wa’adin ba.

A sakon tes da ya turawa ‘yan Najeriya, CBN ya nanata matsayarsa na haramta amfani da tsoffin kudin daga ranar 31 ga Janairun bana.

Kara karanta wannan

Cin Hancin N1bn Ya Jawo Hon. Gudaji Kazaure Ya Tona Asirin Abin da ke Faruwa a CBN

CBN ta sake magana game da sabbin kudi da tsoffi
CBN Ya Aika Sakonnin Tes Ga ’Yan Najeriya Kan Batun Tsofaffin Naira, Ya Gargadi Bankuna | Hoto: Getty Images
Asali: UGC

CBN ta shawarci ‘yan Najeriya su ziyarci shafin yanar gizonsa don karin bayani

Sakon da ya tura na cewa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Kada ku jira har sai ranar 31 ga Janairu, 2023 kafin ku kai tsoffin N200, N500 da kuma N1,000 zuwa banki ko ga wakilan banki.”

CBN ya ce, duk wanda ke neman karin bayani, ya gaggauta hawa shafin yanar gizon babban bankin don fahimtar sabbin bayanai.

Wannan lamari dai na zuwa ne a daidai lokacin da CBN ya daura agogon wa’adi a shafinsa, inda yace saura akalla kasa da kwanaki 14 domin kakkabe karbar sabbin kudi.

Agogon tunin da bankin ya sanya a shafinsa na yanar gizo yana zama tuni ne ga ‘yan Najeriya da su gaggauta daukar matakin rabuwa da tsoffin kudaden.

Sauran bankuna a kasar nan sun dauki salo irin na CBN wajen yiwa ‘yan Najeriya tuni kan batun da ke da alaka da sabbin kudin.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Fadi Wadanda Zai ba Mukamai da Abin da Zai Yi Kafin Kwana 100 a Aso Rock

Babu guda babu ja da baya kan batun wa’adin daina karbar tsoffin kudi

Ya zuwa yanzu dai babban bankin ya ce ba zai janye batunsa na wa’adin karbar tsoffin kudaden ba, wanda ya kasance 31 ga watan Janairun da muke ciki.

Sai dai, har yanzu ‘yan Najeriya na ci gaba da nuna halin ko-in-kula da wa’adin na CBN, wanda a zatonsu za a kara wa’adin zuwa wani lokaci daban.

A bangare guda, bankuna na ci gaba da yiwa ‘yan Najeriya gargadi kan adana kudade; sabbi ko tsoffi don gujewa asara a nan gaba kadan.

Ya kamata 'yan Najeriya su ankara, babu dadi asara, inji masani

Legit.ng Hausa ta tattauna da wani masanin tattalin arziki, kuma dalibin PhD a wata jami’ar kasar waje, Morshood Shuaibu, wanda yace ya kura ‘yan Najeriya basu dauki batun sauyin sun sanya a zukatansu ba.

A cewarsa:

“Maganar gaskiya, kamar mutane gani suke za a kara wa’adi, kaddara za a kara wa’adin, ba daidai bane ka tari aradu da ka wajen ci gaba da rike tsoffin kudi ba, domin kana rike dasu ne babu tabbas.

Kara karanta wannan

Takarar 2023: Yadda Tinubu, Atiku, Kwankwaso da Obi Za Suyi Yaki a Kan Kuri’un Kano

“A shawari na, ina ganin kamata ya yi a ce matukar kana da kudin nan a kasa, ka gaggauta kai su banki, ka ci gaba da tiransfa ko amfani da wayar hannu wajen biya, ga su ATM da POS.
“A yau ko shagon mai shayi yana da POS, to ina dalilin rike tsabar kudi a hannu? Don Alllah ina kira ga ‘yan uwa na ‘yan Najeriya, mu kula.”

Har yanzu dai ana ci gaba da kai ruwa rana tsakanin gwamnan CBN da hukumomin kasar nan kan batun da ya shafi kayyade kudi da buga sabbin Naira.

Asali: Legit.ng

Online view pixel