Labaran tattalin arzikin Najeriya
Wani malamin cocin Dunami a Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom ga tausayawa masu zuwa ibada cocinsa bisa wahalhalu da tsadar rayuwar da aka shiga a ƙasar nan.
Tsohon shugaban kasar Najeriya, Cif Olusegn Obasanjo ya nemo wa kasar hanyar fita daga matsalar tsadar kaya inda ya ce a nemi shawarar kasar Zimbabwe.
Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Plateau ya dira kan tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari kan nakasa tattalin arzikin Najeriya kafin mika ta ga Tinubu.
Gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa aiki ya yi nisa wajen fara rabon hatsi tan 42,000 kamar yadda Shugaba Bola Tinubu ya yi alƙawari a cikin wannan makon.
Babban bankin Najeriya ya kuduri aniyar dakile hauhawar farashin kayayyaki, kuma zai cire wasu makudan kudi kimanin naira tiriliyan 5 daga bankunan kasar.
Asusun ba da lamuni na duniya IMF ya fitar da jerin kasashe 10 mafi arziki a Afirka da aka shiga shekarar 2024 tare da fitar da Najeriya daga jerin.
Jama’an gari sun sace abinci da aka tarwatsa wurin ajiyan kaya a birnin Abuja. Bisa dukkan alamu jami’an tsaro ba su ankara da wuri ba ko kuwa ba a iya kai dauki ba.
Najeriya ta shiga jerin kasashe ma fi annashuwa da jin dadi a Afrika, kuma ita ce ta 8 a jerin kasashe ma fi rayuwa cikin farin ciki da jin dadi a Afrika.
'Yan kabilar Igbo a jihar Kwara sun bayyana kukansu kan yadda aka kakaba musu haraji a kasuwa, lamarin da ya jawo suka yi zanga-zanga a jihar ta Kwara.
Labaran tattalin arzikin Najeriya
Samu kari