Bayan Sulhu da Daurawa, Gwamna Abba Ya Hango Babbar Nasara 1 da Za a Iya Samu a Kano

Bayan Sulhu da Daurawa, Gwamna Abba Ya Hango Babbar Nasara 1 da Za a Iya Samu a Kano

  • Gwamnatin Kano ta bayyana shirinta na ƙara yawan kuɗin shigar da take tarawa duk wata daga N2bn zuwa N10bn
  • Shugaban hukumar tara kuɗin shiga ta Kano (KIRS), Sani Dambo, ne ya faɗi haka a wurin taron hukumar haraji karo na 154 a Abuja ranar Laraba
  • Ya ce kundin bayanai na da matuƙar muhimmanci a kudirin da suka sanya a gaba, yana mai cewa Kano tana da sahihin kundi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano karƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, ta bayyana kudirinta na ƙara yawan kuɗaɗen shiga zuwa N10bn a kowane wata.

Hukumar tara kudaden shiga ta Kano (KIRS) ta ce za ta yi kokarin ɗaga kuɗaɗen shiga na cikin gida a jihar daga N2bn da ake samu yanzu zuwa Naira biliyan 10.

Kara karanta wannan

Majalisa ta buƙaci Shugaba Tinubu ya gaggauta kawo ƙarshen ƴan bindiga a Jihar Arewa

Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano.
Gwamnatin Abba Ta Fara Hangen Tara Kuɗin Shiga N10bn a Wata a Jihar Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Twitter

Shugaban hukumar KIRS, Sani Dambo, ne ya faɗi wannan buri a wurin taron hukumar haraji (JTB) karo na 154 wanda aka yi a birnin Abuja ranar Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dambo, wanda a kwanan nan ya kama aiki kan mukamin bayan wani dan lokaci, ya nuna yadda suke hangen nasara a tattara kuɗaɗen shiga, jaridar Leadership ta rahoto.

Legit Hausa ta faimci cewa jihar Kano ta samu kudin shiga N2.6bn a watan Janairun 2024 amma har yanzun ba a bayyana alƙaluman kuɗin watan Fabrairu ba.

Nawa hukumar ke harin tarawa a Kano nan gaba?

Da yake bayyana kwarin guiwar samun ci gaba a ɓangaren, shugaban KIRS ya ce burinsa na gaba shi ne na samar da kusan Naira biliyan 5 a kowane wata.

"Idan komai ya tafi daidai zamu iya haɗa kudin shiga har Naira biliyan 10 a kowane wata guda," in ji Dambo.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun buɗe wa mutane wuta, sun kashe mutum 7 ƴan gida 1 da wasu bayin Allah

Ya kuma jaddada muhimmancin samar da ingantaccen kundin bayanai domin cimma wannan manufa da hukumar ta sa a gaba, rahoton Blueprint.

"Muna da cikakkun bayanai, kuma abin da muke bukata yanzu shi ne mu ci gaba da sabunta shi.
"Daya daga cikin abubuwan da ke ƙara yawan kudaden shiga shi ne gyara da haɓaka kundin bayanai, saboda zai taimaka wajen faɗaɗa yawan haraji."

- Sani Dambo.

Wannan kalamai na shugaban KIRS na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan an samu sulhu tsakanin babban kwamandan Hisbah, Sheikh Aminu Daurawa da Gwamna Abba.

BUK ta karrama Abba Gida-Gida

A wani rahoton kuma Jami’ar Bayero ta Kano ta karrama Gwamna Abba Yusuf bisa namijin kokarinsa na daga darajar ilimi a jihar

Makarantar ta karrama gwamnan ne a bikin karramawa da yaye dalibai karo na 38 da ya gudana a jami'ar a ranar 2 ga watan Maris, 2024

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262