PDP Ta Samu Baki Yayin da Gwamnanta a Arewa Ya Dira Kan Buhari, Ya Fadi Illar da Ya Yi Wa Najeriya

PDP Ta Samu Baki Yayin da Gwamnanta a Arewa Ya Dira Kan Buhari, Ya Fadi Illar da Ya Yi Wa Najeriya

  • Gwamna a jam’iyyar PDP ya dira kan tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari kan nakasa tattalin arzikin Najeriya
  • Gwamna Caleb Mutfwang ya caccaki Buhari kan yadda ya siyar da kasar tare ruguza tattalin arzikin kasar gaba daya
  • Caleb ya bayyana haka ne yayin rantsar da hadimai 22 a jiya Litinin 4 ga watan Maris a gidan gwamnati da ke Jos a jihar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Plateau – Gwamna Caleb Mutfwang ya koka kan yadda tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya lalata Najeriya.

Caleb ya ce Buhari ne ya rugurguza tattalin arzikin kasar kafin mika mulki ga Shugaba Bola Tinubu wanda yanzu ‘yan kasar ke shan wahala.

Kara karanta wannan

Falgore: Kungiya ta nemi alfarma wajen Abba yayin da Kwankwaso ya samu mukami

Buhari ya sake shiga matsi bayan an tona asirin yadda ya ruguza Najeriya
Gwamna Caleb ya ce Buhari ya kashe kasa kafin mika ta ga Tinubu. Hoto: Muhammadu Buhari, Caleb Mutfwang.
Asali: Facebook

Menene Gwamna Caleb ke cewa kan Buhari?

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin rantsar da hadimai 22 a gidan gwamnatin jihar da ke birnin Jos a jihar Filato, cewar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Muftwang ya ce Buhari ya bar tattalin arzikin Najeriya cikin mawuyacin hali ga Tinubu wanda ya na bukatar lokaci kafin gyarawa.

“Muna cikin wani yanayi a wannan lokaci sai dai ya kamata mu manta da siyasa bayan zabe, mu maida hankali wurin mulkin jama’a.
“Duk Gwamnatin Tarayya ba jam’iyya daya muke ba, amma dole zan fada muku gaskiya, wannan gwamnatin ta gaji tattalin arziki mafi muni tun 1999.
“Gwamnatin ta gaji tattalin arziki wanda ake buga takardun kudi har tiriliyan 30 don a raba su.”

- Caleb Mutfwang

Duk da 'barnar' Buhari, akwai abinci a Filato

Gwamnan ya ce dukkan wannan faduwar darajar naira ba wani abu ba ne illa gwamnatin baya ta siyar da burace-buracen ‘yan Najeriya a kasar, cewar Daily Post.

Kara karanta wannan

An lalata komai a jiha ta amma ba zan yi korafi ba, gwamna a Najeriya ya fadi abin da zai yi a kai

“Babu mamaki kuji ana zanga-zanga a can da nan, mutane na kwacen abinci, mun godewa Allah a Filato muna da abinci fiye da sauran jihohi.
"Ina addu’ar kada lokaci ya zo da ‘yan Filato za su fuskanci wannan matsalar kan abinci, ya nuna dole mu koma mu yi aiki sosai.”

- Caleb Mutfwang

Gwamna Caleb ya dawo da ma’aikata

Kun ji cewa Gwamna Caleb Mutfwang ya dawo da ma’aikata fiye da dubu uku bakin aikinsu bayan dakatar da su.

Gwamnan ya dauki wannan matakin ne bayan dakatar da ma’aikatan da aka yi saboda daukarsu aiki ba bisa ka’ida ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel