Hukumar yan sandan NAjeriya
Rikici ya kaure tsakanin wasu masu baban bola da mutanen unguwar Byazhin da ke kauyen Kubwa a karamar hukumar Bwari da ke babban birnin tarayya Abuja.
Rundunar ƴan sandan Kano ta bayyana cewa Shafi'u Abubakar ya aikata laifin da ake zarginsa na ƙona masallaci ne saboda nuna fushin kan rabon gadon gidansu.
'Yan sanda sun tabbatar da cewa matashin da ya babbaka masallata a kauyen Gezawa ya yi amfani da bam wajen aikata ta'adin. Amma an gano ba harin ta'addanci ba ne.
Wani mutum da ba a gane ko waye ba, ya kone wani masallaci a garin Larabar Abasawa da ke yankin karamar hukumar Gezawa a jihar Kano. Har yanzu babu wanda ya rasu.
Rundunar haɗin guiwa da ta kunshi sojoji, ƴan snada, dakarun ƴan sa'kai na Radda da mafarauta sun yi nasarar ceto fasinjoji 17 daga ƴan bindiga a jihar Katsina.
Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa labarin akwai bullar rashin tsaro a jihar ba gaskiya ba ne, kamar yadda mataimakin Gwamna, Aminu AbdulSalam Gwarzo ya ce.
Wasu ƴan banga sun cafke wani matashi da bam daure a cikinsa yana kokarin tayarwa a garin Dadin Kowa da ke Jos ta Kudu a jihar Plateau a jiya Litinin.
Kwamishinan 'yan sandan Kano ya bayyana cewa daurarru kimanin 400 dake gidan yarin kurmawa a Kano ba su san makomarsu ba. Da yawansu takardar tuhumarsu ta bata.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kani, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce ƴan sanda sun yi kokarin raba faɗan da ya kaure tsakanin ƴan daba a Tarauni.
Hukumar yan sandan NAjeriya
Samu kari