Manyan Labarai A Yau
Dakarun sojojin Najeriya da ke aikin wanzar da zaman lafiya a juhar Katsina, sun samu nasarar kubutar da wasu tarin mutane da 'yan ta'adda suka ƴi garkuwa da su.
Wasu miyagun 'yan bindiga dauke da miyagun makamai sun kai hari a wani kauyen jihar Kogi. 'Yan bindigan sun halaka mutum hudu a yayin harin da suka kai.
Tsohon Gwamnan Zamfara ya zama gwarzon Ministoci. Kungiyar matasa ta ce a duk ministocin da Bola Ahmed Tinubu ya nada, babu mai kokari kamar Bello Matawalle.
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa za ta ba tawagar 'yan wasan Najeriya ta Super Eagles gagarumar kyauta kan nasarar da suka samu ta zuwa wasan karshe a AFCON 2023.
Mataimakin shugaban kasar Najeriya, Kashim Shettima ya taya ‘yan Super Eagles murna bayan nasarar da suka samu kan Afrka ta Kudu a gasar AFCON 2023 a ranar Laraba.
'Yan ta'addan Boko Haram dauke da muggan makamai sun kai sabon harij ta'addanci a jihar Yobe. 'Yan ta'addan sun halaka mutum uku ciki har da wani jami'in dan sanda.
A jiya ne masoya harkokin wasanni a Najeriya suka shiga cikin makoki yayin da wani fitaccen dan jaridan wasanni Kayode Tijani ya rasu bayan fama da jinya a asibiti.
Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS), ta tabbatar da kama wani mai fataucin mutane tare da da ceto wasu mutum uku a hanyarsu na tsallaka boda zuwa Libya.
Farashin Dala yana tashi kullum-yaumin kuma kudin Najeriya yana rasa darajarsa a kasuwa. EFCC ta fara cafke masu cin mutuncin Naira da karbar Daloli babu dalili.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari