Bayan Rikici Ya So Raba Jam'iyyar 2, Jam'iyyar APC Ta Zabi Sabon Shugaba

Bayan Rikici Ya So Raba Jam'iyyar 2, Jam'iyyar APC Ta Zabi Sabon Shugaba

  • Jam'iyyar APC a jihar Benue ta yi sabon muƙaddashin shugaba wanda zai ci gaba da shugabancinta
  • Samun sabon shugaban na zuwa ne a taron da majalisar zartaswar jam'iyyar da aka gudanar a gidan gwamnatin jihar
  • A taron an amince da naɗin Benjamin Omakolo a matsayin muƙaddashin shugaba biyo bayan dakatarwar da kotu ta yi wa shugaban jam'iyyar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Benue - A daren ranar Laraba ne kwamitin zartarwa na jam’iyyar APC na jihar Benue ya amince da naɗin Benjamin Omakolo a matsayin shugaban riƙo na jam’iyyar.

Taron wanda ya gudana a tsohon daƙin liyafar cin abinci na gidan gwamnati ya ci gaba da kasancewa har zuwa ƙarfe 10:45 na dare, wanda gwamnan jihar, Rabaran Hyacinth Alia ya jagoranta, cewar rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP ta bayyana makudan kudaden da aka sace a gwamnatin APC

APC ta yi sabon shugaba a Benue
Jam'iyyar ta yi sabon mukaddashin shugaba a jihar Benue Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

Kwamitin zartaswar jam'iyyar na jihar ya ƙunshi ɓangaren zartaswa na jiha, manyan shugabannin majalisar dokokin jihar, kwamitin gudanarwa na jiha da shugabannin jam’iyyar a ƙananan hukumomi da sakatarorinsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

APC ta yi sabon shugaba a Benue

Da yake jawabi, Gwamna Alia ya bayyana cewa taron wanda shi ne ya ce a gudanar da shi, an kira shi ne domin cike giɓin da aka samu sakamakon dakatar da shugaban jam’iyyar na jiha, Austin Agada da shugabannin jam'iyyar a gundumarsa ta Ihaje suka yi.

The Sun ta ce tun da farko, sakataren tsare-tsare jam'iyyar a jihar, James Orgunga, ya koka kan yadda jam’iyyar ta shiga ruɗani tun bayan dakatar da shugaban jam’iyyar da kuma umarnin kotu wanda ya hana shugaban gudanar da ayyukansa.

Ya ƙara da cewa na ɗan wani lokaci an saɓa wa tanadin kundin tsarin mulkin jam’iyyar na gudanar da tarukan kwamitocin zartaswa na jiha wanda gwamna zai jagoranta.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP ta zargi gwamnan PDP da salwantar da N144bn, ta kawo hujja

Rigima Ta Ƙara Tsananta a Jam'iyyar APC

A baya rahoto ya zo cewa rigimar cikin gida da ake fama da ita a jam'iyyar APC reshen jihar Benue ta ƙara tsananta.

Rikicin ya ƙara tsananta ne biyo bayan samun mutum biyu waɗanda ke ayyana kansu a matsayin shugabamnin jam'iyyar a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel