Manyan Labarai A Yau
Majalisar wakilai ta amince da kudurin da yake neman a binciki jami'an ma'aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya da ke da hannu s badakalar samo digirin bogi.
Dan takarar gwamnan jam'iyyar PDP a zaben gwamnan jihar Ogun na ranar 18, ga watan Maris 2023, Ladi Adebutu, ya samu beli bayan an gurfanar da shi a gaban kotu.
Rundunar ƴan sandan jihar Bauchi, ta bayyana cewa ta samu nasarar gano wasu tarin muggan makamai da aka ɓoye a ƙaramar hukumar Ningi da ke jihar.
Gwamnaton tarayyar Najeriya karkashin jagorancin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ta shirya karya farashin kayan abinci a kasar nan don talaka ya huta.
Tawagar 'yan wasan Najeriya ta Super Eagles za su kara da takwarorinsu na Bafana Bafana na kasar Afirika ta Kudu a wasan neman zuwa wasan karshe a gasar AFCON 2023.
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta sanar da samun nasrar halaka wani kasurgunin shugaban 'yan bindiga a birnin tarayya Abuja. An kuma raunata wasu da dama.
Shugaba Bola Tinubu ya dawo gida lokacin da ake fama da tsadar rayuwa, lamarin da ya jawo zanga-zanga a wurare. Tinubu ya bada umarni tun daga Faransa kafin ya dawo.
Majalisar dattawa ta shirya ganawa da hafsoshin tsaron kasar nan kan matsalar rashin tsaro da ake ci gaba da fama da ita a sassa daban-daban na kasar nan.
Uwargidan shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, Remi Tinubu ta kwantar da hankulan da ƴan Najeriya kan halin matsin da ake ciki a ƙasar nan. Ta ce sauƙi na tafe.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari