Manyan Labarai A Yau
Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke GRA a Sabon Garin Zariya, ta umarci sayar da kadarorin tsohon ɗan takarar gwamnan Jihar Kaduna, Hon. Muhammad Sani Sha’aban.
A ranar Laraba, Sanata Aminu Tambuwal ya tuna haduwarsu ta karshe da Herbert Wigwe yayin da majalisar dattawa ta bukaci a gudanar da bincike da kyau kan hatsarin.
Wata kungiya ta al'ummar Rano, Kibiya da Bunkure ta bukaci Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano da ya yi watsi da batun rushe masarautun jihar da aka kafa.
Wani sojan Najeriya da ya samu rauni a fagen daga yayin kare martabar Najeriya, ya soki matakin Tinubu na ba 'yan wasan Super Eagles kyaututtuka masu gwabi.
Ana zaman dar-dar a Zamfara biyo bayan kashe Magaji Lawal, wani makusancin Sanata Kabir Marafa da wasu jami'an tsaro da aka kaddamar kwanan nan suka yi a jihar.
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Ezenwo Wike, ya sanya tukuicin N20m domin a cafko wasu rikakkun masu garkuwa da mutane da suka addabi birnin.
Wani mutumi ya ce ya je kasar Dubai domin zama tare da abokinsa, amma da ya isa filin jirgin sama, sai ya gano cewa abokin nasa ya kashe wayarsa.
Rahotanni sun bayyana cewa wata gobara da ta tashi a wurin kasuwanci na 'Computer Village' da ke jihar Legas ta jawo asarar dukiya mai tarin yawa.
Jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya, reshen jihar Legas sun kai samame wuraren da ake aikata laifuka, sun yi ram da mutane 400 da ake zargin masu laifi ne.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari