Manyan Labarai A Yau
Wani mai fafutuka, Toyin Raheem, ya roki shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya yi murabus daga kujerar shugaban kasar Najeriya. Ya koka da halin da al'ummar kasar ke ciki.
Gwamnatin tarayya ta hannun karamar ministar kwadago da samar da aikin yi, Nkeiruka Onyejeocha, ta gana da kungiyoyin kwadago na NLC da TUC kan shirin yajin aiki.
An yi ta yaɗa wani hoton a kafafen sada zumunta wanda yake nuna cewa gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya gina wani katafaren gida ana cikin halin matsi a kasa.
Gwamnatin jihar Kano ta hannun hukumar karbar korafe-korafen jama'a da yaki da cin hanci da rashawa, ta fadi dalilin rufe wasu rumbunan boye abinci.
Tsohon sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Boss Mustapha, ya bayar da shaida a gaban kotu kan zargin fitar da $6.2m daga asusun CBN da ake yi wa Godwin Emefiele.
Shugaban bankin Access, Herbert Wigwe, na daga cikin sanannun 'yan Najeriyan da suka rasa ransu a hatsarin jirgin sama. Mun tattaro muku wasu daga cikin sauran.
Majalisar dattawan Najeriya ta shiga ganawar sirri da hafsoshin tsaro a zauren majalisar da ke Abuja, kan matsalar rashin tsaron da ake fama da ita a kasa.
Bayo Onanuga, mai ba Shugaba Tinubu shawara kan yada labarai da dabaru, ya bayyana cewa Najeriya kasa ce matalauciya wacce arzikinta bai kai inda ake kai sa ba.
Primate Elijah Ayodele, ya gargadi Shugaban kasa Bola Tinubu game da rikcin tattalin arziki. Ya yi hasashen cewa dala za ta kai N1700 sannan buhun shinkafa N90,000.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari