Manyan Labarai A Yau
Kujerar mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu ta shiga tangal-tangal yayin da majalisar dokokin jihar ta fara shirin tsige shi daga kan mukaminsa.
Wani dalibin makarantar sakandiren gwamnati da ke birnin tarayya Abuja, ya rada ransa. Dalibin ya bar duniya ne bayan ya taka wayar wutar lantarki.
Hamshakan attajiran Najeriya guda biyu, Aliko Dangote da Femi Otedola za su gina gidajen ma'aikata da dakunan kwanan dalibai a makarantun shari'a Najeriya.
Rahotanni sun samu kan rasuwar shugaban jam'iyyar APC na jihar Ekiti, Mista Paul Omotoso. Marigayin ya yi bankwana da duniya ne a safiyar ranar Laraba.
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bayyana dalilin da ya sa tsohon gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ya yi nasara kan PDP a zaben gwamnan jihar na 2020.
Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya tuna da 'yan majalisar dokokin jihar yayin da ya gwangwaje su da sabbin motoci. Gwamnan ya ce yana so su ji dadin yin aiki.
Fadar shugaban kasa ta fito ta yi magana kan rahotannin da ke yawo dangane da batun cire takunkumin hana 'yan Najeriya biza da kasar UAE ta yi a baya.
Tsagerun 'yan ta'addan Boko Haram sun yi awon gaba da mata 'yan gudun hijira har mutum 319 a wani sabok farmaki da suka kai a jihar Borno ta Najeriya.
An samu barkewar wani rikici a jihar Legas wanda ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutane da dama a yankin Ibeshe na jihar. 'Yan sanda sun shiga lamarin.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari