Labarin Sojojin Najeriya
Wasu rahotanni sun ce hukumar EFCC da NFIU sun fara bincike kan yadda aka so amfani da wasu kudi a shirin kifar da gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Cocin HEKAN a Kaduna ya tabbatar da cewa an kashe Fasto Yahaya Kambasiya tare da sace mutane sama da 20 a wani sabon harin da ’yan bindiga suka kai a Jihar Kaduna.
A labarin nan, za a ji cewa rundunar tsaron kasar nan ta yi sauye-sauye da dama, inda aka canjawa manyan sojoji akalla 67 wuraren aiki bayan nada hafsoshin tsaro.
Fadar shugaban kasa ta gargadi 'yan Najeriya kan yada labarun juyin mulki marasa tushe. Nayo Onanuga ya ce yada labarin zai jawo bata sunan Najeriya a duniya.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bukaci hafsoshin tsaro su zage damtse su magance barazanar tsaron da ke kara taaowa a wasu sassan kasar nan.
Rahotanni daga rundunar sojin Najeriya na nuna cewa sojojin da aka tsare kan zargin shirya juyin mulki a Najeriya sun karu zuwa 42, ana ci gaba da bincike a kansu.
Wata jarida ta kara tattaro bayanai kan sojoji 16 da ake zargin hukumomi sun tsare su ne bisa zargin hannu a shirin juyin mulkin da bai yi nasara ba.
A labarin nan, za a ji cewa hukumomin tsaron kasar nan sun yi aiki tare wajen bin wasu kudi da aka samu dangatawa da kokarin kifar da gwamnatin Bola Tinubu.
Sabon shugaban sojin saman Najeriya, Sunday Kelvin Aneke ya bayyana cewa zai kai hana 'yan ta'adda sakat a Najeriya ta yadda za su gagara zama su kitsa kai hari.
Labarin Sojojin Najeriya
Samu kari