Labaran garkuwa da mutane
Wasu tsagerun ƴan bindiga sun hallaka mutum 5 ƴan gudun hijira a masallaci a kauyen Katapko da ke yankin ƙaramar hukumar Toto a jihar Nasarawa ranar Alhamis.
Rundunar ƴan sanda reshen jihar Kano ta tabbatar da cafke wani da ake zargin kasurgumin ɗan garkuwa da mutane ne a yankin ƙaramar hukumar Dawakin Kudu.
Kotun daukaka kara mai zama a Lagos ta tabbatar da hukuncin da aka yankewa Baale na Shangisha, Magodo, ta rage masa shekaru 3 daga cikin shekaru 15.
Hajiya Hauwa’u Adamu, mahaifiyar fitaccen mawakin nan Dauda Kahutu Rarara ta godewa ɗaukacin al'ummar da suka taimaka da addu'a lokacin da aka sace ta.
Yan fashin daji sun shiga kauyen Kurmin Kare a karamar hukumar Kachia ta jihar Kaduna, sun kashe dagajin kauyen, Ishaya Barnabas kana suka tafi da mutum 3.
Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya bayyana dalilin da ya sanya ake samun karuwar matsalar rashin tsaro a jihar. Gwamnan ya ce laifin ta'ammali da kwayoyi ne.
Rahotannin da muke samu yanzu na nuni da cewa mahaifiyar fitaccen mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara ta kubuta daga hannun 'yan bindiga bayan sati uku.
Rundunar ƴan sanda reshen jihar Akwa Ibom ta tabbatar da cewa wasu ƴan bindiga sun yi garkuwa da direba da fasinjoji 18 a kan titi a jihar Akwa Ibom.
Rundunar 'yan sandan jihar Legas ta yi ram da wasu iyayen da su ka sa dansu a kasuwa domin su samu kudin ficewa daga kasar nan saboda matsin rayuwa.
Labaran garkuwa da mutane
Samu kari