'Yan Bindiga Sun Buɗe Wa Matafiya Wuta, Sun Yi Awon Gaba da Mutane da Yawa a Titin Abuja

'Yan Bindiga Sun Buɗe Wa Matafiya Wuta, Sun Yi Awon Gaba da Mutane da Yawa a Titin Abuja

  • Ƴan bindiga sun tare wata motar Sharon a titin Abuja zuwa Lokoja, sun yi awon gaba da fasinjoji masu yawa zuwa cikin daji
  • Wani direba da abun ya faru a kan idonsa ya bayyana cewa da kyar ya samu nasarar tsira daga harin ƴan bindigar
  • Mamban kungiyar NURTW, Ɗanjuma Suleiman ya ce ƴan bindigar da sun sako mutum shida daga cikin waɗanda suka ɗauka a harin

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Wasu ‘yan bindiga sun harbe wani direban bas har lahira tare da yi awon gaba da fasinjoji 16 a kusa da kauyen Chikara da ke kan hanyar Abuja zuwa Lokoja.

Jaridar Daily Trust ta samu labarin cewa lamarin ya faru ne a ranar Alhamis da ta gabata da misalin karfe 12 na tsakar dare.

Kara karanta wannan

Ambaliya a Dubai ta halaka dan shekara 70, an yi mamakon ruwan sama

IGP Kayode.
Yan sanda sun tare motar Bas a titin Abuja-Lokoja, sun tafi da mutane Hoto: Nigerian Police Force
Asali: Facebook

Yadda lamarin ya faru

Ƴan bindigar sun fara da buɗe wa motar bas ɗin kirar Sharon wuta a kusa da gidan gonar Yakwo kafin daga bisani su aikata ɗanyen aikin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An tattaro cewa maharan sun kashe direban bas din nan take, yayin da suka yi awon gaba da wadanda ke cikin motar ciki har da wata uwa mai shayarwa, zuwa cikin daji.

Wani direban motar bas ta haya, Saidu Ibrahim, ya ce:

"Ina tafe a bayan motar bas ɗin da lamarin ya faru da ita, amma bisa ikon Allah babu wata mota a bayana, saboda haka na yi maza na taka birki, na juya da gudu kuma na tsira."

Mutum 6 sun kuɓuta

Danjuma Suleiman, mamban kungiyar direbobi ta kasa (NURTW) reshen Abaji, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce shida daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su, da suka hada da mata biyu da wata uwa mai shayarwa, sun kuɓuta daga hannun maharan daga baya.

Kara karanta wannan

Farashin man fetur ya ragu a wasu gidajen mai yayin da Dala ta ƙara karyewa a Najeriya

"A wannan daren, shida daga cikin wadanda aka ɗauka sun shaƙi ‘yanci yayin da masu garkuwan suka gano cewa daya daga cikin su, wata uwa mai shayarwa, ba ba zata iya tafiya a daji ba," in ji shi.

Suleiman ya ci gaba da cewa wadanda lamarin ya rutsa da su sun taso ne daga jihar Delta da nufin zuwa birnin Lafia a jihar Nasarawa.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Kogi, SP Williams Ovey Ayah, bai dauki kiran waya ko amsa sakon tes da aka aika masa kan lamarin ba.

A rahoton Leadership, ƴan bindiga na yawan kai hari titin Lokoja da ke cikin jihar Kogi, suna yin garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa.

Yan bindiga sun kashe sakataren PDP

A wani rahoton na daban Yan bindiga sun harbe sakataren jam'iyyar PDP na ƙaramar hukumar Tsafe, Musa Ille, har lahira a jihar Zamfara ranar Litinin.

Shugaban jam'iyyar PDP na Tsafe, Garba Garewa, ne ya tabbatar da haka ranar Talata, ya ce maharan sun harbe shi a ƙofar gidansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel