Katsina
Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bar Abuja bayan ya mika mulki ga Asiwaju Bola Ahmed Tinubu. Ya shiga jirgin soji zuwa Katsina a hanyarsa ta zuwa Daura.
A ranar Litinin, 29 ga watan Mayu ne aka rantsar da zababben gwamnan jihar Katsina, Dikko Umar Radda akan mulki. Dikko shi ne tsohon daraktan hukumar SMEDAN.
Shugaba Buhari ya ce ya matsu ya koma Daura da ke jihar Katsina bayan ya gama mulkinsa a yau Litinin 29 ga watan Mayu, ya ce zai koma ne don kula da dabbobinsa.
Daura ta na shirya gagarumar maraba ga Muhammadu Buhari da zai bar Aso Rock. Za ayi bukukuwa da wasanni da nufin karrama Buhari wanda ya yi shekaru 8 a ofis.
'Yan sanda a jihar Katsina ta tabbatar da kama wasu da ake zargi da fasa shaguna tare da satar wayoyin hannu guda 48, sun ba da tabbacin kama daya matashin.
Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina ya naɗa sabon mataimakin shugabam jami'ar Umaru Musa Yar'adu da sabon shugaban kwalejin fasahar Hassan Usman Katsina.
Ana fargabar cewa shugaban yan bindiga, Dan-Karami ya yi hijira da tawagarsa daga Zamfara ya dawo jihar Katsina saboda gujewa luguden wuta da sojoji ke musu.
Uwargidan tsohon shugaban kasa, Umaru Musa Yar'adua ta bayyana cewa tsohon shugaban bai taɓa son yin siyasa ba. Ta ce babban burin Yar'adua shine zama malami.
Matar tsohon shugaban kasan Najeriya ta bayyana cewa, mijinta ba dan rashawa bane, kuma bai neman mata hakazalika baya shan giya ko aikata wata alfasha a kasa.
Katsina
Samu kari