Kasashen Duniya
Tsohon firaministan Isra'ila, Ehud Barak, ya caccaki Benjamin Netanyahu kan yakin da ake yi da Iran. Ehud Barak ya zargi Netanyahu da yin karya kan yakin.
Binciken sojin Isra'ila ya tabbatar da cewa kuskuren lissafi ne ya sa dakarun ƙasar suka harba makaman atilare kan wani manomi maimakon mayakan Hezbollah.
Gwamnatin Iran ta fitar da wani bidiyo da ke nuna wani rumbun ajiyar makamai a karkashin kasa. An tanadi makamai masu linzami a karkashin kasa a Tehran.
Shugaban kungiyar NATO, Mark Rutte ya sanar da cewa kasashe 22 da suke kungiyar da wasunsu sun fara magana kan duba yiwuwar bude mashigar Hormuz da Iran ta toshe.
Firanministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya nemi kasashen duniya su taya shi yakin da ya ke yi da Iran bayan kai manyan hare-hare zuwa yankin Arad.
Hukumar IEA ta bayyana cewa ci gaba da yakin Iran, Amurka da Isra'ila zai jawo gagarumar matsala ga makamashi a fadin duniya yayin da ake ci gaba da gwabza yaki.
Amurka ta fito fili ta fadawa Isra'ila cewa yaki da Iran zai dauki lokaci mai tsawo kafin a kawo karshensa. Wani rahoto ya ce yakin zai iya kaiwa Satumban 2026.
Harin da Iran ta kai a Isra’ila ya jawo ta ayyana dokar ta-baci bayan harin makamai, ta rufe makarantu, wuraren aiki tare da hana tarukan jama’a domin tsaro.
Ministan kudin Amurka, Scott Bessent, ya yi tsokaci kan batun ci gaba da daukar nauyin yaki da Iran ta fuskar kudade. Ya yi watsi da batun kara haraji.
Kasashen Duniya
Samu kari