Dangote da Adenuga Sun Shiga Jerin Attajiran Duniya da Suka Tafka Asarar Sama da $1.4trn a 2022

Dangote da Adenuga Sun Shiga Jerin Attajiran Duniya da Suka Tafka Asarar Sama da $1.4trn a 2022

  • Karshen 2022 bata zo wa da attajiran duniya da dadi ba, ciki kuwa har da jiga-jigai na Amurka, Rasha da China
  • A cewar wani sabon rahoto, attajiran duniya sun yi asarar $1.4trn a cikin shekarar da ta gabata; 2022
  • Ba a bar Aliko Dangote da Adenuga ba, domin kuwa sun ga raguwar arziki cikin watanni 12 na 2022

A cewar rahoton Bloomberg, attajiran duniya sun ga raguwar arziki a cikin shekarar 2022 da ta gabata.

Rahoton ya bayyana cewa, raguwar arzikin attajiran na zuwa ne daga tasirin annobar Korona da ta shafi duniya.

Misali, irinsu Elon Musk, Jeff Bezos, Changpeng Zhao da Mark Zuckerberg sun rasa jumillar $392bn a hade.

Dangote da Adenuga sun yi asarar kudi a 2022
Dangote da Adenuga Sun Shiga Jerin Attajiran Duniya da Suka Tafka Asarar Sama da $1.4trn a 2022 | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Elon Musk kadai, ya rasa $25.8bn a ranar 27 ga watan Janairun bara bayan da kamfaninsa na Tesla Inc. ya sanar da tsaiko a harkallarsa.

Kara karanta wannan

Ashe babu dadi: Kasurgumin dan bindiga ya firgita, an rusa gidansa, an kashe yaransa 16

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shine karo na hudu da aka samu mummunan ragi mai zurfi a jerin dukiyar attajirai na jaridar Bloomberg.

Nawa ne attajiran Rasha suka rasa?

Attajiran kasar kasar Rasha sun yi rashin $46.6bn a jumillance a ranar 24 ga watan Fabrairu, ranar da kasar ta mamaye Ukraine.

Yayin da gamayyar Turai, Burtaniya da Amurka suka sanya takunkumi kan jiga-jigan Rasha da kasuwancinsu, ya ba manyan ‘yan kasuwar kasar wahalar shigar da kayayyakinsu ga kasashen Turai.

Nawa attahiran China suka rasa?

Akalla $64.6bn attajiran kasar China suka rasa a ranar 14 ga watan Maris din bara, kuma har yanzu suna ci gaba da fama.

A yakin tabbatar da Korona ta daina yaduwa, harkar gine-gine da fasaha mai daukar hankali sun rasa kusan $164bn a shekarar 2022.

Rashin da attajiran Najeriya suka yi

A bangaren Najeriya, attajirin dan kasar da ya hau jerin attajirai na Boomberg ne rahotonsa ya fito fili karara.

Kara karanta wannan

Fitattun Yan Najeriya a Turai Sun Daukar Wa Atiku Gagarumin Alkawari Gabannin 2023

Jerin attajiran ya nuna a ranar Juma’a 30 ga watan Disamban 2022 cewa, Dangote ya mallaki $18.7bn, ragin $421m da yake dashi a farkon shekarar.

Sai dai, rahoton Forbes ya ruwaito cewa, Dangote ya mallaki $12.5bn ya zuwa ranar Juma’a 30 ga watan Disamban bara, idan aka kwatanta da $12.7bn a farkon shekarar.

Wannan na nufin, a cewar rahoton Forbes, Dangote ya yi rashin $2m ne kacal daga dukiyarsa a 2022.

Haka nan, rahoton Forbes ya ce, Mike Adenuga na daga cikin attajiran Najeriya uku da suka shiga jadawalinsa, kuma ya samu faduwa a dukiyarsa, Abulsamad Rabiu ya hau matsayinsa.

A farkon 2022, Adenuga ya mallaki $6.6bn, wanda a yanzu kuma yake da $5.6bn, dukiyarsa ta ragu da $1bn.

Attajirin Najeriya ya kara arziki

A nasa bangaren, Abdulsamad Rabiu ya tsallake matakai masu yawa tare da samun $3.4 a watanni 12 na shekarar 2022.

Forbes ta ruwaito cewa, Abdulsamad a yanzu yana da tarin kudi har $7.8bn, wanda a farkon shearar 2022 abin da yake dashi duka $4.4bn ne.

Kara karanta wannan

Shekarar 2022 Ta Zama Shekarar Zulumi Da Fargaba, Akalla Mutum 8,000 Ne Suka Rasa Ransu a Shekarar

Abdulsamad dai na ta tashe a shekarun nan, akwai yiwuwar ya kwace matsayin Dangote nan ba da jimawa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel