Jihar Kano
Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, da Sarkin Gaya, Aliyu Ibrahim Gaya sun mika sakon taya murna ga zababben gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf.
Jam'iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, ta bukaci dan takarar APC a zaben gwamnan Kano, Yusuf Gawuna da ya yi ta yan wasa ya taya Abba murnar cin zaben.
Magoya bayan jam'iyyar All Progressives Congress (APC), a jihar Kano, sun ɓarke da zanga-zanga kan nasarar da Abba Gida-Gida ya samu a zaɓen gwamnan jihar.
Abba Kabir Yusuf, zababben gwamnan jihar Kano ya umurci mutanen da ke tattaki a kasa zuwa Kano don taya shi murnar cin zabe su dakata, su yi masa addu'a kawai
Zababben Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya ce bai taba cewa zai rushe wani gini a Jihar ko kuma rushe masarautun da gwamnati mai barin gado ta kirkiro ba.
Dan takarar gwamnan jihar Kano a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar APC, Nasiru Gawuna ya bayyana cewa kamata yayi sakamakon zaben gwamnan jihar ya zama inconclusive.
Sha’aban Sharada bai dauki siyasa da gaba ba, ta taya NNPP samun nasara. A nan aka ji wani ya ce Allah Sarki Sha'aban Sharada ya fadi zabe a watan Shaaban.
Gwamnan Kano sabo, Abba Gida-gida ya bayyana kadan daga abubuwan da ya shriya yiwa Kanawa a kwanaki 100 na farkon mulkinsa. Ya fadi tsarinsa gaba da dayan.
Gwamnatin Ganduje ta bayyana dage dokar hana fita da ta sanya a jihar Kano, inda tace kowa ya ci gaba da harkokinsa na yau da kullu, kamar yadda aka saba kawai.
Jihar Kano
Samu kari