Zaben Gwamnan Kano: “Abun Kunya Ne Kalubalantar Nasarar Abba Gida-Gida” – NNPP Ga APC

Zaben Gwamnan Kano: “Abun Kunya Ne Kalubalantar Nasarar Abba Gida-Gida” – NNPP Ga APC

  • Jam'iyyar NNPP ta shawarci dan takarar jam'iyyar APC a zaben gwamnan Kano da aka yi, Yusuf Gawuna da ya taya Abba Kabir murnar cin zabe
  • Jigon NNPP, Abubakar Yesufu ya ce abun kunya ne kalubalantar sakamakon zaben da APC ke yunkurin yi
  • Yesufu ya ce Abba Gida-Gida na da farin jini sannan ya samu karbuwa a wajen al'ummar jihar Kano

Kano - Kakakin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Abubakar Yesufu, ya bayyana yunkurin da jam’iyyar APC, don kalubalantar nasararsu a zaben gwamnan jihar Kano a matsayin wahalar da kai.

Jam’iyyar NNPP ta kuma bukaci APC da ta taya zababben gwamnan, Abba Kabir Yusuf murna, cewa zaben ya tabbatar da farin jini da karbuwar da dan takararta ya samu.

Zababben gwamnan jihar Kano, Abba Kabir
Zaben Gwamnan Kano: “Abun Kunya Ne Kalubalantar Nasarar Abba Gida-Gida” – NNPP Ga APC Hoto: The Cable
Asali: Facebook

Yesufu ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da aka gabatarwa manema labarai, jaridar Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Murnar lashe zaben PDP: 'Yan daba sun lalata cibiyar gwamnati ta NBTI a wata jihar Arewa

Wani bangare na sanarwar na cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Yunkurin APC na kalubalantar sakamakon zaben gwamnan kora-kunya da hauka ne, aikin banza ne da kuma wani yunkurin lullube rashin kunya da barnar da Mallam Yusuf Gawuna da abokansa suka shirya a lokacin zaben gwamna a jihar Kano.
"Mun yaba ma zababben gwamna, Abba Kabir Yusuf kan wannan nasara wanda ya cancanci samu. Don haka muna kira ga Yusuf Gawuna da ya zama dan wasa ta hanyar taya wanda ya yi nasara murna. Duk da dabarun da aka yi amfani da su wajen yi masa murdiyar kuri'u fiye da miliyan 1,200 da kuri'u 890 da Gawuna ya samu ta hanyar runto, dan takararmu ne ya lashe zaben.
"Shakka babu takarar ya kasance tsakanin mai iko amma mara farin jini Mallam Yusuf Gawuna, mataimakin gwamna mai ci da mara iko amma shahararre Abba Kabir Yusuf na NNPP.

Kara karanta wannan

Lauje cikin nadi: Dan takarar gwamnan NNPP a Arewa ya ce bai amince da sakamakon zabe ba, zai tafi kotu

"Nasarar mutane ne a kan mulkin zalunci. A wannan gabar, muna jinjinawa baturen zabe, Farfesa Doko Ibrahim, shugaban jami'ar Ahmadu Bello, kan jajircewa, kin yarda ayi murdiya da kuma tsayawa tsayin daka a kan adalci da gaskiya."

Ban taba cewa zan rushe masarautun Kano ba - Zababben gwamna Abba Kabir

A wani labarin kuma, mun ji cewa zababben gwamnan jihar Kano, ya karyata rade-radin da ake yi cewa zai rushe masarautun gargajiya na jihar da gwamnati mai ci ta kirkiro.

Da yake ce bai taba fadin haka ba a iya lokacin da ya dauka yana yakin neman zabe, Abba ya ce wannan duk zance ne kawai da masu kuntun kashi a tsuluyarsu suka kirkira.

Asali: Legit.ng

Online view pixel