Malamin addinin Musulunci
A labarin nan, za a ji cewa Reno Omokri ya bayyana cewa akwai abubuwan da Nasir El-Rufa'i ya aikata a jihar Kaduna a lokacin da ya ke gwamna, ya cancanci kamu.
Kungiyar MUSWEN da malaman Musulmi a Kudu maso Yamma sun jaddada bin umarnin Sarkin Musulmi kan azumin Ramadan 2026, suna tabbatar da hadin kai da zaman lafiya.
Gwamnatin Tarayya ta kasa gabatar da umarnin kotu kan tsare Sheikh Sani Abdulkadir Zaria da ake zargi da shirin juyin mulki, kotun ta dage shari'a zuwa Juma'a.
Wani jigo a jam'iyyar APC, Dr. Sani Zangina ya caccaki majalisar shari'ar Musulunci kan kiran sai an cire sabon shugaban INEC, Joash Amupitan daga mukaminsa.
Malaman musulunci a jihar Kwara sun ja hankalin musulmi su yi taka tsan-tsan da abubuwan da za su yi a kafafen sada zumunta idan azumin Ramadan ya kama.
Futaccen Fasto a Najeriya, Elijah Ayodele, zai kaddamar da sabon masallaci da ya gina shi kaɗai a ranar Asabar, 14 ga Fabrairu, 2026 da muke ciki.
Hajiya Naja'atu Muhammad ta soki Sheikh Isa Pantami, inda ta kira shi makaryaci a shirin Ali Jita. Ta kuma soki tsarin zaben Najeriya da ta kira na 'kama karya.'
Tsohon shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan, ya gargadi Musulmi su yi aiki tare wajen dakile rashin tsaro da ke haddasa tashin hankali a Najeriya.
Farfesa Abdullahi Saleh Usman ya yi murabus daga mukamin Shugaban NAHCON, yana mai cewa shawarar ta samo asali ne daga dalilai na kashin kai kawai.
Malamin addinin Musulunci
Samu kari