Ramadan: Mai Alfarma Sarkin Musulmi Ya Fitar da Sanarwa Mai Muhimmanci Ama Saura Kwana 30 Azumi

Ramadan: Mai Alfarma Sarkin Musulmi Ya Fitar da Sanarwa Mai Muhimmanci Ama Saura Kwana 30 Azumi

  • Sarkin Musulmi ya buƙaci a fita duban jinjirin watan Sha'aban 1445AH daga lokacin da rana ta faɗi ranar Asabar, 29 ga watan Rajab
  • Za a fara duba jinjirin wata na 8 a jerin watannin musulunci daga yau Asabar 10 ga watan Fabrairu, 2024 yayin da ya rage kwana 30 a fara azumin Ramadan
  • Kwamitin ganin wata na fadar Sarkin Musulmi ya roƙi duk wanda ya ga jinjirin watan ya tura saƙo ta hanyoyin da aka tanada

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Mai alfarma sarkin Musulmai a Najeriya, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya roƙi ɗaukacin al'ummar Musulmi su fara duban jinjirin watan Sha'aban daga yau Asabar.

Sultan na Sakkwato ya buƙaci a fara duba jinjirin watan Sha'aban na shekarar 1445AH daga ranar Asabar, 29 ga watan Rajab, 1445AH (10 ga Fabrairu) bayan faɗuwar rana.

Kara karanta wannan

Bayan lashe zaɓe, ƴan majalisa sun zaɓi sabon shugaban majalisar dokoki a jihar Arewa

Mai alfarma sarkin Musulmi, Alhaji Sa'aɗ Abubakar na III.
Ramadan: "Ku Fara Dugan Jinjirin Watan Sha'aban" Sultan Ga Musulmin Najeriya Hoto: Daular Usmaniyya
Asali: Twitter

Majalisar koli ta harkokin addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA) karkashin Sarkin Musulmi ce ta fitar da wannan saƙo a wata sanarwa da aka wallafa a shafin kwamitin ganin wata na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka zalika, mataimakin darakta janar na NSCIA, Farfesa Salisu Shehu, ya tabbatar da haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Jumu'a.

Saura kwana nawa a fara azumin watan Ramadan?

Legit Hausa ta fahimci cewa wannan wata da Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya bada umarnin a fita duba wa shi ne wata na takwas a jerin watannin Musulunci.

Kuma hakan na nufin watan azumin Ramadan mai tarin albarka (wata na 9 a jerin watannin musulunci) ya kara kusantowa domin bai wuce a ce saura kwana 30 ba.

A sanarwan da Farfesa Shehu ya fitar, ya ce:

"A kimiyance, lokacin da ake tsammanin watan zai gama haduwa shi ne ranar Juma'a, 9 ga Fabrairu, 2024 da karfe 11:59 na dare.

Kara karanta wannan

Majalisar Dattawa ta titsiye gwamnan babban banki CBN kan muhimmin batu, bayanai sun fito

"Yana da mahimmanci a lura cewa wata yana bayyana kuma ana iya ganinsa yawanci na tsawon lokaci (har ma yana ɗauke da wasu abubuwa) bayan ya kammala haɗuwa."

A ƙarshe, kwamitin duban wata na fadar Sarkin Musulmi ya buƙaci duk wanda ya ga jinjirin watan ya gaggauta tura saƙo ta hanyoyin da aka amince da su.

Gwamna Yahaya ya yi ta'aziyya

A wani rahoton kuma Gwamna Inuwa Yahaya ya yi alhinin rasuwar jagoran ɗarikar Tijjaniyya a jihar Gombe, Khalifa Sheikh Muhammadu Kobuwa ranar Jumu'a.

Fitaccen malamin addinin musuluncin ya rasu ne da safiyar ranar Jumu'a, 9 ga watan Fabrairu, 2024 kuma tuni aka masa jana'iza.

Asali: Legit.ng

Online view pixel