Tsadar Mai
Shugaban Izalah bangaren Jos ya bukaci Shugaba Tinubu ya dawo da tallafin mai don samun sauki ga al’umma inda ya ce 'yan kasar su na cikin wani hali.
Yayin da ake fama da tsadar kaya musamman bangaren siminti, Gwamnatin Tarayya za ta yi zama da Alhaji Aliko Dangote da Abdussamad Rabiu kan tsadar siminti.
Tsohon shugaban Najeriya a mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya yi magana kan halin da ake ciki inda ya bai wa hukumomi shawarar dakile matsalar.
Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya saka ma’aikata hawaye a jihar yayin da ya amince da tsawaita biyan kudaden rage radadin cire tallafi har na watanni shida.
Mai fafutukar kafa kasar Yarbawa, Sunday Igboho ya kare gwamnatin Bola Tinubu bayan Sarkin Musulmi ya soki gwamnatin da cewa ta bar komai ya lalace a kasar.
Mota ta murkushe wani matashi mai suna Jamilu, a ranar Talata a lokacin da yake yunkurin tserewa da kayan abincin wata mata a kasuwar Kwali da ke a Abuja.
Tinubu ya amince da nadin sabbin shugabannin hukumomin NAFDAC da kuma NCDC a yau Alhamis 15 ga wata Faburairu yayin da ake cikin wani hali a kasar.
Majalisar Wakilan Najeriya ta bukaci saka tallafi a harkar jigilar maniyya aikin hajji saboda muhimmancinsa ga addinin Muslunci da kuma tsadar rayuwa da ake ciki.
Shugaba Bola Tinubu zai tafi kasar Habasha don halartar babban taron kungiyar Nahiyar Afirka (AU) a karo na 37 a birnin Addis Ababa da ke kasar a gobe Alhamis.
Tsadar Mai
Samu kari