Tsadar Mai
Bankin Duniya ya fitar da sabon rahoto kan yunwa da za a sake shiga a jihohin Arewacin Najeriya guda bakwai saboda rashin tsaro a wannan shekara da muke ciki.
Jigon jam’iyyar APC kuma tsohon kwamishina a jihar Kano, Ilyasu Musa Kwankwaso ya yabawa matakin fitar da abinci da Shugaba Tinubu ya yi a wannan mako.
Kungiyar ‘yan kasuwa a jihar Yobe, UMAPO ta koma ga Allah tare da gudanar da salla ta musamman don neman taimako daga ubangiji kan wannan tsadar rayuwa
Yayin da ake ci gaba da shan fama a Najeriya, Ministan Albarkatun Noma, Abubakar Kyari ya ce watakila a rufe iyakar Najeriya kan tsadar abinci a kasar.
Ministan watsa labarai, Mohammed Idris, ya ce shirin da gwamnati ta yi ba fitar da tan dubu 42 na masara, gero da garri zai karya farashin kayan abinci a kasuwanni.
Yayin da ake cikin mawuyacin hali, Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar ya bukaci hukumar ICPC d daukar mataki kan masu boye kayayyakin abinci a Najeriya.
Gwamnatin jihar Neja karkashin jagorancin Gwamna Mohammed Umar Bago ta bada umarnin sakin Aisha Jibrin, jagorar zanga-zangar nan da aka yi a Minna.
Shugaban hukumar karbar korafe korafe da yaki da cin hanci a Kano, Barista Muhuyi Magaji ya sha alwashin fara kai samame runbunan ajiyar kayan abinci.
Tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar APC a Arewa maso Yamma, Salihu Lukman ya caccaki jami'yyar kan halin da ake ciki na wahalar tsadar rayuwa da kunci.
Tsadar Mai
Samu kari