Tiantian Kullander, Wanda Ya Kirkiro Crypto Ya Mutu A Shekaru 30

Tiantian Kullander, Wanda Ya Kirkiro Crypto Ya Mutu A Shekaru 30

  • Allah ya yi wa Tiantian Kullander, wanda ya kafa kamfanin kudin crypto mai suna Amber rasuwa yana da shekaru 30
  • Rahotanni sun bayyana cewa Kullander ya rasu ne a cikin barcinsa a ranar 23 ga watan Nuwamba, ya bar matar aure da yara
  • Kullander ya kafa kamfanin Amber ne a shekarar 2017 tare da wasu masana a harkar banki kuma ta bunkasa har sunansa ya shiga jerin 'Forbes 30 under 30'

Tiantian Kullander, matashin da ya kafa kamfanin kudin intanet wato 'Crypto' mai suna Amber Group, ya yi mutuwar rashin tsammani, a cikin barcinsa a ranar 23 ga watan Nuwamba, rahoton Sahara Reporters.

Kullander wanda aka fi sani da 'TT' ya kafa kamfanin Amber a shekarar 2017 tare da wasu masana harkar banki, ciki har da tsaffin ma'aikatan Goldman Sachs Group da Morgan Stanley, New Telegraph ta rahoto.

Kara karanta wannan

Daga Twitter: Matashi ya jefa kansa a matsala, ya shiga hannu bayan zagin Aisha Buhari

Tiantian Kullander
Tiantian Kullander, Wanda Ya Kirkiro Crypto Ya Mutu A Shekaru 30. Hoto: Sahara Reporters.
Asali: Facebook

Kafin wannan lokacin, ya yi aiki a matsayin mai hada-hadar kudi a kamfanonin biyu, kuma a 2019 an ayyana shi cikin jerin sunayen Forbes 30 Under 30, wanda ke karrama matasan yan kasuwa da masu kamfanoni.

Amber ta yi ta'aziyyar rasuwar Kullander

Kamar yadda Daily Mail ta ruwaito, sanarwar da kamfanin ta fitar ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ya saka zuciyarsa da ruhinsa a kamfanin, a kowanne mataki na girmansa. Ya yi jagoranci da misali ta hanyar basirarsa, kyauta, kan-kan da kai, jajircewa da hazaka."

Sanarwar ta cigaba da cewa:

"TT shugaba ne wanda ake girmamawa kuma ana masa kallon yan farko a masana'antar. Zurfin iliminsa da son hadin gwiwa da kokarin taimakawa wasu su bunkasa ya taimakawa sabbin kamfanoni da mutane da dama.
"Hangen nesansa da hazaka ya karfafawa mutane, ayyuka da kamfanoni da dama gwiwa."

Kara karanta wannan

Hoton Sauyawar Yaron Da Ke Aikin Karen Mota a Baya, Ya Hadu Da Biloniya Tony Elumelu

Kullander ya rasu amma abin da ya gina zai cigaba da rayuwa - Amber

Sanarwar ta kara da cewa baya da zama daya cikin wadanda suka kafa Amber da 'gina shi zuwa kamfanin hada-hadar kudi na biliyoyi' TT kuma mamba ne na kwamitin amintattu na Fnatic - daya daga cikin kamfanonin wasanni na intanet mafi bunkasa a duniya - wanda KeeperDAO ya kirkira.

"Abin da TT ya bari zai cigaba da rayuwa kuma za mu yi aiki tukuru don ganin Amber ta zama jagorar masana'antar mu, domin wannan shine buri da faran TT.
"TT miji ne na gari, mahaifi mai kaunar yayansa kuma aboki na gari. Rasuwarsa abin bakin ciki ne kuma muna mika ta'aziyya ga iyalansa tare da masa addu'a."

Shugaban Binance da wasu attajiran Crypto ke fuskantar karayar arziki

A bangare guda, kun ji cea masu crypto da wadanda suka sha romonta suna cikin wani hali mara dadi.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Shahararren Mawakin Bishara Na Najeriya Ya Yanke Jiki, Ya Mutu A Gidansa A Legas

A 'yan shekarun baya-bayan nan, masana a bangaren fasaha sun zama attajirai ta hanyar sayar da kadarorin su na zamani ta yanar gizo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng