Allahu Akbar: Yawan Mabiya Addinin Islama Ya Karu a Kasar Ingila
- Jama'ar Ingila na ci gaba da karbar addinin Islama, kaso da yawa ya karu cikin kasa da shekaru 10 da suka gabata
- Rahoton da muka samo ya bayyana adadin kason da ya karu cikin shekaru 10, kamar yadda kididdigar 2021 ta nuna
- Addinin Islama na ci gaba da karbuwa a duniya, kullum karin kaso ake samu mai tsoka a bangarori daban-daban na duniya
Landan - Al'ummar Musulmi ta samu karuwa yayin da wata kididdiga ta bayyana irin kasuwar da adadin Musulmai ya yi matukar karuwa a kasar Ingila.
Kididdigar ta 2021 ta bayyana cewa, Musulmai sun karu daga kaso 4.9% zuwa 6.5% a shekarar da ta gabata.
Wannan na fitowa ne daga rahoton kidayar da aka yi ta hanyar tambayar mazauna kasar addini, asali da kuma addinin da suke bi.
A cewar ofishin kidayar, kasar na gudanar da irin wannan kididdiga ne duk bayan shekaru 10, rahoton BBC Hausa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Yadda kididdigar ta kasance
Wannan lamari ya zo da kafa tarihi, domin kuwa a wannan karon addinin kirista ya samu raguwa sosai a turai, musamman a Ingila da Wales.
Rahoton kididdigar ya bayyana cewa, a yanzu dai addinin kirista ya yi kasa daga kaso 59.3% a 2011 zuwa kaso 46.2% na shekarar da ta gabata.
A bangare guda, mulhidai, ko kuma wadanda ke cewa babu ruwansu da addini sun karu zuwa kaso 37.2% na al'mmmar yankin.
Hakazalika, kididdigar ta nuna akwai mabiya addinan Hindu, Sikh Budda da kuma Yahudawa, kamar yadda jaridar The Guardian ta ruwaito.
A bangaren al'adu kuma, Burtaniya na da dandazon mutanen Asia da sauran nahiyoyin duniya da ke rayuwa a kasar, kuma sun samu shaidar tabbacin zama da kuma cikakkun 'yan kasa.
Ba na sallah, bana zuwa coci, bana bautar gungu, inji farfesa a Najeriya
A Najeriya kuwa, wani farfesa Wole Soyinka ya bayyana matsayinsa game da addini da kuma bautar ubangiji a rayuwarsa.
Wole Soyinka ya bayyana cewa, bai damu da bin addini ba ko kadan saboda wasu dalilai da ya bayyana a wurin wani taro.
Soyinka dai sananne ne a duniya a harkar rubuce-rubuce, kuma ya kasance abin tunawa a duniyar adabin Turanci.
Asali: Legit.ng