Jama’a Sun Shiga Mamakin Yadda Ake Siyar da Tsintsiyar Kwakwa N11,200 a Turai

Jama’a Sun Shiga Mamakin Yadda Ake Siyar da Tsintsiyar Kwakwa N11,200 a Turai

  • Wani mai siyar da kayayyakin amfanin gida a kasar Amurka ya jawo cece-kuce yayin da ya fadi farashin tsintsiyar kwakwa a kasar
  • Tsintsiyar da ake siyarwa N100 a Najeriya ta kai sama da N11,200 a kasar waje kamar yadda mutumin ya nuna
  • Jama'ar intanet sun gaza hakuri, sun tofa albarkacin bakinsu ga abin da ya faru, sun kuma shiga mamaki matuka

Wani Ba'amurke ya girgiza jama'a yayin da ya nuna farashin tsintsiyar kwakwa a kasar waje.

A wani hoton da aka yada a Instagram, an ga tsintsiya gama gari irinta Najeriya ana siyar da ita a farashin $14, kusan N11,200 kenan, lamarin da ya sa jama'a luguden lebe.

Yayin da wasu ke caccakar mai siyar da kayan da kwankwatsa tsada kan jama'a, wasu kuwa sun yi kokarin fahimtar yadda lamurra suke a duniya, musamman tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Kofin Duniya: Bashir El-Rufai Yayi Kira ga Hukumomin Qatar da su Kama, gurfanarwa da halaka duk wanda ya kai giya filin wasa

Tsiniyar da ake rainawa a Najeriya ta fi karfin talaka a Turai
Jama'a sun shiga mamakin yadda ake siyar da tsintsiyar kwakwa N11,200 a turai | Hoto: @mufasatundeednut
Asali: Instagram

A tun farko, Mufasatundeednu ne ya yada hoton tare da cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Aaaaaaaaaaaaah! $14 = N11,200. Nawa ne ainihin kudin tsintsiyar nan? Mutane na samun kudi kawai a Amurka."

Abin da jama'a ke cewa

Dah_freshdeltaboi yace:

"Hauka ne abin."

Comedianebiye yace:

"Wannan zai share kowace mace daga kafafunta."

Obaksolo yace:

"Wannan zai hada ya share har da kaddara a hade."

Globalwalex yace:

"Wannan abin dubawa ne, a wurinku shara ce, saboda a Afrika ne ba ta da daraja, idan za mu kai irin wannan da yawa, farashin dala zai sauka. Idan wakokinmu za su sanu a duniya, me zai hana kayayyakinmu."

Justgoddy yace:

"A unguwarmu N100 take, idan na budewa mai siyarwa ido zai bani a N50."

Pepepretti_herself yace:

"Na taba siya £50 fa. N20 ake siyarwa a kauyenmu."

Kara karanta wannan

Duk Wanda Yace 2023 Lokacinsa ne, Ya Tafka Babban Kuskure, Kwankwaso Yayi Gugar Zana

Bombastigal yace:

"Sabuwar kasuwata kenan jama'a idan kuna bukatar tsintsiya zan zo Landan na kawo muku na samu kasuwar da zan ci."

Mrsucessguy yace:

"Za ka iya amfani da ita wajen shara da kuma yin miyar ewedu shi yasa ta yi tsada."

_jozzy_of_lagos_ yace:

"Tsinsiyar rayuwa ce? Shin tsintsiyar za ta share matsalolin mutum ne? Shin za ta share dukkan muggan shugabannin Najeriya? Idan ba ta yi ba, ba zan siya ba."

Yadda ake siyar da jaka 'Ghana Must Go' a farashin N860k

A wani labarin, a kasar waje an ce ana siyar da jakar tafiya a farashin da ya haura N800,000, lamarin da ya jawo cece-kuce a intanet.

Wata kafar yanar gizo ce aka gani ta sanya allon farashin da ya nuna kudin jakar mai kama da 'Ghana Must Go'.

Mutane sun bayyana kaduwa tare da yin martani mai zafi kan wannan lamarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel