Nade-naden gwamnati
Attajirin dan kasuwa, Abdulsamad Rabiu ya ki karban tayin zabarsa da aka yi domin ya shiga kwamitin kudi da gwamnatin Shugaban kasa Tinubu ta kafa.
Al'ummar Musulmi a jihar Plateau sun yi martani kan alakarsu da Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Plateau inda su ka ce ba ya nuna mu su wariya a jihar.
Sabon shugaban ma'aikatan jihar Kano, Musa Abdullahi ya gargadi ma'aikatan jihar da su guji zuwa wurin aiki a latti inda ya kafa musu lokacin zuwa aiki.
Ministar jin kai da walwalar jama'a, Dakta Betta Edu ta samu mukamin shugaban kwamitin ministoci a kungiyar ECOWAS bayan amincewar Bola Ahmed Tinubu.
Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya nada Alhaji Abdullahi Musa a matsayin sabon shugaban ma'aikata bayan yin murabus din Alhaji Usman Bala daga mukaminsa.
Bola Ahmed Tinubu, shugaban kasa a Najeriya ya kuma amincewa da naɗin mutum biyu a matsayin manyan sakatarorin ma'aikatar kuɗi da ma'aikatar albarkatun mai.
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sake naɗa Mele Kyari a matsayin shugaban kamfanin mai na kasa NNPCL da mambobin gudanarwa guda takwasa ranar Litinin.
Tsohon ministan sufuri a Najeriya, Rotimi Amechi ya bayyana cewa ya tafka kuskure yayin da ya tura sunan Wike mukamin Minista a lokacin mulkinsa a jihar Ribas.
Bola Tinubu ya nada mutane 10 da za su jagoranci MOFI. Dr. Shamsudeen Usman ya zama Shugaban majalisar sa ido shi kuma Dr. Armstrong Ume Takang shi ne CEO.
Nade-naden gwamnati
Samu kari