Yan bindiga
Wasu 'yan bindiga masu garkuwa da mutane sun sace dalibai da malamai a wata makaranta a jihar Neja bayan sace wasu da dama a jihar Kebbi da kai hari Kwara.
Sanata mai wakiltar Abia ta Arewa a majalisar dattawa, Uzor Orji Kalu, ya bayyana cewa akwai dalilin da ya sanya Mai girma Bola Tinubu bai je jihar Kebbi ba.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya umarci karamin ministan tsaron kasa Bello Matawalle ya koma Kebbi domin sa ido kan batun sace dalibai mata 24 a Maga.
Wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci a jihar Sokoto. Miyagun sun hallaka mutane tare da sace iyaye mata da jariran da suke shayarwa.
Ƴan bindiga sun sake kai hari Kwara, inda a wannan karon suka farmaki manoma a kauyen Bokungi, tare da sace hudu daga ciki. Wannan na zuwa bayan harin coci.
Tsohon ministan sadarwa, Farfesa Ali Isa Ibrahim Pantami, ya koka kan hare-haren da aka yi fama da su a wasu sassan kasar nan. Ya bukaci hukumomi su tashi tsaye.
Gwamnatin Kwara ta rufe makarantu a kananan hukumomi huɗu saboda barazanar tsaro, bayan harin ’yan bindiga a cocin Eruku. Gwamna ya nemi kafa sansanin sojoji.
Matasa a Eruku, Kwara sun toshe hanyar Ilorin–Kabba bayan harin ’yan bindiga da ya kashe mutane uku, tare da garkuwa da wasu 10 a cocin CAC Oke-Isegun.
Wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci kan mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba a jihar Sokoto. Sun yi awon gaba da mutane.
Yan bindiga
Samu kari