Yan bindiga
Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace tsohon ɗan Majalisar Dokokin Jihar Ogun, Hon. Maruf Musa, a ƙaramar hukumar Ogun Waterside.
Rundunar tsaron jihar Ondo watau Amotekun ta kama wasu mutane 39 da suka ce sun gudo ne daga yankin jihar Sakkwato, ana zargin sun tsere ne daga harin Amurka.
Wasu 'yan bindiga sun kai hari kan Fastoci biyu mabiya darikar Katolika a Mararaba da ke Nasarawa, kusa da Abuja, inda suka daba musu wuka da dare.
Wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai kazamin hari a jihar Kebbi. Ana fargabar mutane da dama sun rasa rayukansu. Wasu da dama sun tsere zuwa daji.
Dakarun sojojin saman Najeriya sun kai hare-hare kan maboyar 'yan ta'adda a jihar Zamfara. Sojojin sun kashe tsageru masu yawa tare da lalata sansanin 'yan bindiga.
Mayawakan kungiyar 'yan ta'addan ISWAP sun kai farmaki wasu yankunan jihar Yobe sun raunata basarake sun sace mutane kwanaki bayan harin kasar Amurka.
Dakarun sojoji sun samu nasara kan 'yan bindiga a jihar Kano. Sojojin sun yi arangama da 'yan bindigan ne bayan da suka kawo hari a karamar hukumar Shanono.
'Yan bindiga sun kashe 'yan gida daya su biyu tare da sace mutane 4, ciki har da matar Alhaji Yayaji da yaransa, a wani hari da suka kai kauyen Pindiga a Gombe.
Dakarun soji sun ceto mutum ɗaya a iyakar Kano da Katsina, yayin da aka kashe 'yan ta'adda 438 tare da ceto mutane 366 a yankin Arewa maso Gabas cikin watanni bakwai
Yan bindiga
Samu kari