Yan bindiga
Rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta sanar da samun nasarar ceto mutum 100 da aka yi garkuwa da su tare da hallaka miyagun 'yan bindiga mutum biyar.
Wasu miyagun 'yan bindiga sun kai mummunan farmaki a jihar Kogi inda suka hallaka mutane da dama tare da kona gidaje masu tarin yawa a yayin harin.
Wasu miyagun yan bindiga da ake zargin fulani makiyaya ne sun halaka.mutane sama da 20 a wani sabon hari da suka kai wani kauye a jihar Kogi ranar Jumu'a.
Da misalin karfe 1 na daren ranar Juma'a aka ruwaito wasu 'yan bindiga sun farmaki masu zuwa sallar Tahajjud a kauyen Kuta da ke Minna, babban birnin jihar Neja.
Kungiyar Southern Nigeria Youth Movement ta ja kunnen Gwamna Dauda Lawal kan sukar Bello Matawalle inda ya ce ya kamata ya maida hankali kan dakile matsalar tsaro.
Dakarun tsaron Najeriya sun fitar da jerin sunayen kasurguman 'yan bindiga da suka hallaka da irin nasarorin da suka samu a yaki da ta'addanci a Arewacin Najeriya
Gwamnatin jihar Zamfara ta dauki matakin takaita zirga-zirga a tsakanin iyakokinta da jihohin Sokoto da Katsina. Ta dauki wannan matakin ne saboda rashin tsaro.
Jami'an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), rundunar 'yan sanda da 'yan bijilan sun kai samame mabuyar 'yan bindiga a jihar Filato, sun kashe akalla 'yan ta'adda 18.
Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar hallaka 'yan ta'adda guda biysr a jihar Taraba bayaɓ sun yi musayar wuta. Sun kuma yi nasarar kwato makamai masu yawa.
Yan bindiga
Samu kari