Dandalin Kannywood
Malam Ali a Kwana Casa’in zai yi shekaru 2 bai fito a wasan kwaikwayo a Kano ba. Tauraron ya yi suna a dandalin sada zumunta na zamani na Tik Tok .
Mawakan Kannywood sun kai wa Buhari ziyara a gidansa da ke Daura, sun nuna goyon bayansu gare shi. Hakan na zuwa jima kadan bayan da mawaki Rarara ya caccaki Buhari.
Fitacciyar jarumar masana'antar Kannywood, Rashida Adamu Abdullahi Mai Sa'a za ta auri sahibinta, Alhaji Aliyu Adamu, Sardaunan matasan Gwoza a tanar Asabar.
Fitaccen mawakin Hausa Shu'aibu Ahmed Abbas, wanda aka fi sani da Lilin Baba ya ziyarci malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi. Ya ba da gudunmawa ga yan gaza.
A ranar 1 ga watan Nuwamba ne jarumar Kannywood, Hadiza Aliyu Gabon, ta maka wani mutum a kotun Kaduna kan zargin bata mata suna a cikin al’umma.
Fitaccen jarumin fina-finan Hausa ta Kannywood, Sadiq Sani Sadiq ya karyata rade-radin cewa shi dan daba ne a baya. Ya ce shi dai ya yi aikin farauta da kuruciya.
Shahararren jarumi a masana’antar Kannywood, Sadiq Sani Sadiq, ya bayyana cewa yana fatan wannan sana’ar tasa ta yi sanadiyyar shigarsa gidan Aljanna.
Jarumar Radeeya Ismail ta bayyana cewa jarumi Ali Nuhu ne kaɗai za ta iya aura daga cikin gaba ɗaya jaruman da ke masana'antar finafinai ta Kannywood.
Tsohuwar jarumar Kannywood wacce aka fi sani da Sayyada Sadiya Haruna a TikTok, ta kai ƙarar mijinta G-Fresh ƙara a gaban kotu tana neman a raba aurensu.
Dandalin Kannywood
Samu kari